✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ruwa ya yi ajalin wani matashi a Kano

Matashin ya gamu da ajalinsa yayin da yaje wanka a rafi, a ranar Lahadi.

Wani matashi mai kimanin shekaru 25 a duniya ya rasu a sakamakon nitsewa a wani rafi dake kauyen Garin Bature a Karamar Hukumar Bichi a jihar Kano.

Matashin, mai suna Aabnas Abdusalam dai ya gamu da ajalin nasa ne ranar Lahadi yana tsaka da wanka a rafi.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Alhaji Saminu Yusuf ya fitar.

A cewar sanarwar, “Mun samu kiran agajin gaggawa daga wani mai suna Yahuza Muhammad kan lamarin da misalin karfe 2:05 na yamma.

“Ba tare da bata lokaci ba muka aike da jami’anmu don ceto wanda ya fada ruwan.

“Sai dai ko kafin su tsamo shi ya riga ya rasu, amma an ba wa mai garin kauyen Garin Bature, Shu’aibu Isma’il gawarsa domin a yi masa suttura,” inji kakakin.

Sai dai ya ce hukumar ta su na ci gaba da bincike domin gano musabbabin mutuwar matashin.

Kazalika, ya gargadi iyaye da su rika hana yaransu wanka a rafi.