✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ruwa Da Iska Ya Kashe Mace 1 da jikkata Wasu 16 A Gombe

Mutum 16 aka kai sashin agajin gaggawa na asibitin Bajoga sakamakon karaya da raunuka da suka samu.

Wata mata ta rasu, wasu mutum 16 kuma sun samu munanan raunuka a sakamakon ruwan sama da iska mai karfi a garin Bajoga, hedikwatar Karamar Hukumar Funakaye a Jihar Gombe.

Babban likita a babban asibitin garin Bajoga, Dokta Abdulkarim Musa Abba, ya shaida wa Aminiya cewa mutum 16 aka kai sashin agajin gaggawa na asibitin sakamakon karaya da raunuka da suka samu.

Da yake magana kan iftila’in a fadarsa ranar Litinin, Sarkin Funakaye, Dokta Yakubu Mohammad Kwairanga ya bayyana cewa ruwa da iskan da aka samu a karshen makon da ya gabata sun jawo mummunan asara amma sun dauke shi a matsayin kaddara daga Allah.

Sarkin ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta kawo wa mutanen da abin ya shafa dauki, sannan ya yi addu’ar Allah Ya kare na gaba.

Da yake bayyana cewa masarautar ta ziyarci wadanda iftila’in ya shafa a asibiti domin jajantawa da kuma tallafa musu da kudin magami; sarkin ya kuma ja hankalin al’ummar Funakaye da su guji yin gine-gine a kan hanyar ruwa ko zuba shara a magudanan ruwa.

Wuraren da iskar tafi barna sun hada da Makarantar Sakandaren ‘Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya (FGGC Bajoga) inda ta kware rufin azuzuwan da ofisoshi da kuma wasu muhimman wurare.

Hakazalika a babban asibitin garin na Bajoga, manyan turakun wutar lantarki  da suka kai wa asibitin wuta sun karye, sannan transifomarsu ta yi bindiga kuma rufin dakin Yara ya kware.

Aminiya ta zaga wasu sassan cikin garin na Bajoga inda ta gane wa idon ta yadda Iskar tayi ta’adi.