Wani ruwan sama hade da iska mai karfin gaske sun lalata wasu gidaje a garin Damaturu, hedikwatarta Jihar Yobe.
An shafe awa guda ana maka ruwan da iskan, tun gabanin Sallar La’asar a ranar Lahadi.
- An nada sabon Kwamishinan ’yan sandan Kano da wasu 11
- Yadda na sha da kyar a rikicin Hausawa da Gbagyi a Abuja —Dan gwangwan
Da daddare bayan Sallar Isha, aka sake maka wani ruwan kamar da bakin kwarya na tsawon lokaci.
Aksarin gidajen da suka rushe suna unguwanni irin su Fawari na da Nainawa da gefen Rukunin Gidajen Ali Marami sai wani bangare na unguwar Pomfomari da makamantan su.
Wani magidanci da wannan iftila’in ya rutsa da gidansa a unguwar Nainawa, Malam Umar ya tabbatar da cewa, gidan nasa na laka ya rushe kuma a halin yanzu bai san inda zai sa kansa ba, don haka ya nemi mahukuntan jihar da su kawo musu dauki ko sa samu matsuguni.
Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin Shugaban Hukumar agajin gaggawa ta jihar (SEMA) Alhaji Mohammed Goje kan ko suna sane da hakan, kuma wane kokari suke shirin yi don kai dauki ga wadanda abin ya shafa, ya ci tura.