Akalla mutum biyu aka tabbatar da mutuwarsu yayin da wasu mutum uku suka jikkata a sakamakon rushewar wani gini a yankin Alayaki na Jihar Legas.
Bayanai sun ce rushewar benen mai hawa uku wanda ba a kammala gininsa ba ta faru ne a sakamakon mamakon ruwan sama da ya sauka a yankin.
- Batanci: ’Yan sanda sun soma bincike kan rikicin da ya barke a Bauchi
- Shekara 1 da hatsarin jirgin Janar Ibrahim Attahiru
Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa na Jihar Legas, Ibrahim Farinloye ne ya tabbatar da faruwar lamarin.
“Mun ceto mutum uku da ransu sannan kuma akwai guda biyu da rai ya yi musu halinsa, kuma yanzu haka ana ci gaba da aikin ceto,” a cewarsa.
Sai dai Babban Sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa na Jihar Legas, Dokta Olufemi Oke-Osanyitolu, ya ce binciken da aka gudanar a farko–farko ya nuna cewa aikin ginin ya saba wa ka’idodin tabbatar da aminci da ingancin gine-gine.
Jihar Legas ta yi kaurin suna wajen rushewar gine-gine, inda a bayan nan an tafka asarar rayuka da jikkatar mutane da dama kari a kan dukiya da ke salwanta.
Kimanin mutum 10 ne suka rasa rayukansu a ranar Lahadi, 1 ga watan Mayu, a sakamakon rushewar wani gini mai hawa uku a Unguwar Ebute Metta da ke birnin Ikkon na Legas.
Hukumomi a Najeriyar na danganta yawaitar rushewar gine-gine da rashin bin tsarin gini da ma rashin ingancin aiki.