✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rushewar gini Kano: Wutar lantarki ta kashe mai aikin ceto

Mutum biyu sun rasu, an ceto wasu a raye bayan rushewar bene a Kasuwar ’Yan Wayoyi da ke Beirut Road a Kano

An tabbatar da rasuwar mutum biyu sakamakon rushewar wani bene mai hawa biyu a Kasuwar ’Yan Waya da ke Titin Beirut a Kano.

Sakataren Kungiyar Agaji ta Red Kuri’a a Jihar Kano, Musa Abdullahi, ya sanar cewa wani jami’in kamfanin wutar lantarki na KEDCO ya rasu a yayin aikin ceton.

Ya bayyana cewa ma’aikatan na kokarin yanke wuta daga ginin da ya rushe ne, amma aka samu matsala, wutar da aka kashe ta dawo masa, ta yi ajalinsa a nan take.

Ya shaida wa Aminiya a safiyar Laraba cewa an yi nasarar ceto mutum takwas a raye daga baraguzan ginin da ya rushe ranar Talata.

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta tabbatar da ceto mutum tara daga rusasshen ginin.

Kodinetan NEMA a Kano, ya ce an garzaya da mutum takwas din da aka ceto zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Muhammed da ke Kano domin ba su kulawa.

“Sai dai mutum daya daga cikinsu ya rasu a asibiti, shida da suka samu kananan raunuka da kujewa kuma an ba su magani an sallame su, sauran mutum daya kuma ya samu karaya a wurare daban-daban kuma ana ba shi kulawa a asibitin,” in ji shi.