An tabbatar da rasuwar mutum biyu sakamakon rushewar wani bene mai hawa biyu a Kasuwar ’Yan Waya da ke Titin Beirut a Kano.
Sakataren Kungiyar Agaji ta Red Kuri’a a Jihar Kano, Musa Abdullahi, ya sanar cewa wani jami’in kamfanin wutar lantarki na KEDCO ya rasu a yayin aikin ceton.
- Kwankwaso 2023: Ba za mu bi Shekarau PDP ba —Kawu Sumaila
- Najeriya za ta daina sayo fetur daga kasar waje a 2023 —NNPC
Ya bayyana cewa ma’aikatan na kokarin yanke wuta daga ginin da ya rushe ne, amma aka samu matsala, wutar da aka kashe ta dawo masa, ta yi ajalinsa a nan take.
Ya shaida wa Aminiya a safiyar Laraba cewa an yi nasarar ceto mutum takwas a raye daga baraguzan ginin da ya rushe ranar Talata.
Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta tabbatar da ceto mutum tara daga rusasshen ginin.
Kodinetan NEMA a Kano, ya ce an garzaya da mutum takwas din da aka ceto zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Muhammed da ke Kano domin ba su kulawa.
“Sai dai mutum daya daga cikinsu ya rasu a asibiti, shida da suka samu kananan raunuka da kujewa kuma an ba su magani an sallame su, sauran mutum daya kuma ya samu karaya a wurare daban-daban kuma ana ba shi kulawa a asibitin,” in ji shi.