A ranar 17 ga watan Disamban da ta gabata ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhar ya bai wa ’yan Najeriya tabbacin cewa idan zaben shekarar 2023 ya zo zai tabbatar an yi zabe na gaskiya kuma kowa halinsa ne zai kai shi ga nasara ba guguwa ba.
Tun lokacin da Shugaba Buhari ya fara tsayawa takarar shugabancin kasar nan a shekarar 2003 ’yan siyasa suke ta hawa doronsa suna samun nasara a yayin da suka tsaya takarar mukamai daban-daban, tun daga mukamin gwamna zuwa na ’yan Majalisun Tarayya da na jihohi da sauransu.
Haka aka rika tafiya, sai ka ga dan takara ya hada hotonsa da na Buhari domin ya san ta haka ne kawai zai iya samun goyon bayan jama’a saboda tsananin farin jinin da Buhari yake da shi a wurin talakawa, musamman na yankin arewaciin kasar nan. Wannan ya sanya ’yan takara da yawa sun kai bantensu saboda jingina da Buhari da suka yi.
Tun da farko da aka kada kugen siyasa domin komawa mulkin demokoradiyya a kasar nan a shekarar 1998, a lokacin Shugaba Buhari yana shugaban hukumar kula da sarrafa kudin rarar man fetur (PTF) sai ya ajiye aiki ya ce shi ba zai iya aiki da ’yan siyasa ba, amma saboda ’yan siyasa sun san irin kimar da yake da ita a wurin talakawa sai da suka matsa masa ya shiga siyasa har ma ya tsaya takarar shugabancin kasar nan a shekarar 2013, kuma tun daga lokacin ’yan takara suke ta jingina da shi suna samun nasara a zabubbukan da ake yi ba tare da sun kashe kudi mai yawa ko sun fuskanci wata matsala sosai ba, kawai sai ka ga mutum ya zama gwamna ko dan majalisa, guguwar Buhari ta kwashe shi ta kai ga nasara, alhali ba a ma sanshi sosai ba.
Wani abu da ya kara taimaka wa ’yan takaran da suke jingina da Buhari shi ne, kokarin da suke yi su tabbatar Buhari ya daga hannunsu a lokacin yakin neman zabe ya ce wa jama’a ga dan takarar da za su zaba, domin a wancan lokacin idan dai har Buhari ya daga hannun dan takara, musamman a wadansu jihohi da dama na arewacin kasar nan, to ya ci zabe ya gama, domin talakawa suna bin umarnin Buhari sau da kafa ne.
Haka kuma a wancan lokacin ne aka fito da amfani da kalmar ‘sak,’ inda Shugaba Buhari yake umartar magoya bayansa su zabi duk dan takarar da jam’yyarsa ta tsayar, wannan ‘sak’ din ma ta taimaka wajen samun nasarar ’yan takara da yawa a zabubukan da suka gabata. Wata tsohuwa saboda Buhari ya ce idan an zo zabe a yi ‘sak’ daga sama har kasa, sai ta dangwala wa duk jam’iyyun, ta ce Baba Buhari cewa ya yi a yi ‘sak.’
Sai dai kuma a yayin da Buhari yake ta taimaka wa ’yan takara suna kai wa ga nasara, shi kuma sai da ya tsaya takara sau hudu bai kai ga nasara ba, saboda haka ya yi ta ikirarin cewa ya hakura da takara, amma saboda ’yan siyasa sun san shi ne yake taimaka musu suna kai wa ga nasara, sai suka rika matsa masa lamba har sai ya yarda ya sake fitowa takara, domin su ci gaba da hawa doronsa suna kai wa ga nasara.
Bayan ya zama Shugaban Kasa kuma Buhari ya ci gaba da taimaka wa jam’iyyarsa domin ’yan takaran da ta tsayar su kai ga nasara, wanda ya sanya wadansu jam’iyyun adawa ke ganin gwamnati tana taimakawa wajen tabka magudin zabe.
Yanzu dai ga dukkan alamu Buhari ya noke ne yana so ya rama amfani da shi da ’yan siyasa suka yi da shi a shekarun baya suka kai ga nasara kuma suka juya masa baya, don haka tun da shi ma ya samu nasara daga baya har ya samu damar yin wa’adi biyu a matsayin Shugaban Najeriya, to idan zabe ya zo kowa tasa ta fisshe shi, babu sauran batun sak ko guguwa.
Masu fashin-baki na ganin cewa ko da Buhari bai rushe guguwar tasa da kansa ba, ta riga ta rushe, domin ’yan Najeriya da dama sun fara dawowa daga rakiyarsa saboda bai yi musu abubuwan da suke zato zai yi domin su samu saukin rayuwa ba. Shi ya sanya wadansu ke cewa da farko mutane ba su fahimci maganar mawakin nan Rarara ba da yake cewa ‘dodar ta tabbata’ ba sai yanzu, domin kuwa yanzu ne ake dodara musu zafi, talakawa suna ji a jikinsu, kuma wannan ya sanya talakawa ke cewa ashe maganar da Buhari ya fada a shekarar 2011 cewa ‘jiki magayi’ yanzu ne za su ga tabbacin haka.
Shugaba Buhari dai ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa zai tabbatar an gudanar da sahihin zabe na gaskiya da adalci a shekarar 2023, muna fata Allah Ya kai mu lokacin lafiya, Ya kuma ba shi ikon cika alkawarin da ya dauka.