Dambarwar siyasa da ke tsakanin magoya bayan Jam’iyyar APC a Jihar Kaduna ta sake daukar sabon salo a ranar Talatar da ta gabata bayan da Hukumar Kula da Birnin Kaduna (KASUPDA) ta rusa gidan Sanatan Shiyya ta daya da ke Jihar Sanata Sulaiman Othman Hunkuyi da ke kan Titin Sambo.
An bude gidan ne a matsayin sabon ofishin Jam’iyyar APC da danladi Wada ke shugabanta sakamakon rikicin jam’iyyar da aka dade ana fama da shi.
A makon jiya ne bangaren su Sanata Hunkuyi da ba ya ga maciji da bangaren Gwamnan Jihar Malam Nasiru El-Rufa’i suka bude sabon ofishin nasu.
Binciken Aminiya ya gano cewa kwana daya da bude ofishin wadansu matasa da ba a san ko su wane ne ba sun je sun shafa jan fenti a gidan bayan da bangaren danladi Wada ya aike da takardar sammaci ga Gwamnan kan ya bayyana a gabansu don amsa tuhumar aikata wasu laifuffuka da ya yi wa jam’iyyar amma bai je ba, inda hakan ya sa suka fitar da takardar dakatar da Gwamnan daga jami’yyar tare da wadansu mataimakansa.
Sai dai Jam’iyyar APC bangaren gwamnati ta bakin Mukaddashin Sakatarenta Yahaya Baba Pate ta fitar da wata sanarwa inda ta dakatar da Sanata Suleiman Hunkuyi daga jam’iyyar bisa zargin karya dokokin jam’iyyar.
A cewarsa, APC bangaren Sanata Hunkuyi haramtacciya ce don haka ba ta da hurumin da za ta ce ta kori Gwamna ko ta dakatar da magoya bayansa daga Jam’iyyar APC.
Sai dai kuma Mai ba Gwamna EL-Rufa’I shawara a kan harkokin siyasa Uba Sani ya shawarci Sanata Suleiman Hunkuyi ya je kotu idan yana ganin gwamnati ta saba doka wajen rushe gidan nasa.
Uba Sani wanda ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja, ya yi nuni da cewa Hunkuyi ya karya dokar filaye ta hanyar mayar gida zuwa ofis, kuma bai biya harajin kasa ban a tsawon shekara takwas, don haka gwamnati ta kwace filin yanzu za ta mayar da shi wurin shakatawa ne.
Amma Sanata Suleiman Hunkuyi ya bayyana cewa ya biya kudin kasa ga hukumar tara kudin shiga ta jihar Kaduna har zuwa shekarar 2017. Haka kuma ya ce gwamnati ta sake tura masa da wata sanarwa da ke gargadinsa ya biya kudin kasaNaira miliyan 30 na shekara 24 na gidan da yake ciki mai lamba 18a a titin Inuwa Wada ko kuma ta rushe shi.
Kudin kasa na gidan a shekara Naira dubu 61 da 160.9 ne, kuma adadadin kudin da zai biya na shekara 24 Naira miliyan 1 da dubu 467 da 861.6 ne,amma aka hada da tarar Naira miliyan 30, wanda ake bukatar ya biya Naira miliyan 31 da dubu 467 da 861.6 nan da wata guda.
El- Rufa’i ya wuce gona da iri – Sagay
Shugaban Kwamitin Bai wa Shugaban kasa Shawara kan Yaki da Cin hanci da Rashawa (PACAC) Farfesa Itse Sagay (SAN), ya ce Gwamna El-Rufa’i ya wuce gona da iri kan rushe gidan Sanata Hunkuyi da gwamnatinsa ta yi.
Farfesa Sagay ya bayyana haka ne a shekaranjiya Laraba ga jaridar Naij.com, inda ya ce ya ji mamakin Gwamnan wanda yake matukar girmamawa a ce ya sauko kasa haka saboda sabani da sauran ’ya’yan jam’iyyarsa.
Ya ce matakin na Gwamna yana iya wargaza yunkurin samar da zaman lafiya da jagoran Jam’iyyar APC na kasa Asiwaju Bola Tinubu, ke yi bisa umarnin Shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma yana iya illa ga jam’iyyar a zaben badi.
“Ya wuce gona da iri, domin baya ga aikata hakan ba daidai ba ne, kuma zai iya illa ga jam’iyyar a jihar. Ya kamata a yi tunani a kan wadannan abubuwa. Don haka ban ji dadi hakan ba, kuma ina jin kuskure ne,” inji shi.
El-Rufa’i ba zai iya daukar zafin adawar siyasa ba – Hunkuyi
Sanata Sulaiman Hunkuyi ya fitar da wani takaitaccen jawabi kan rusa gidan nasa ta Tiwita inda ya ce rusa gidan nasa alama ce da ke nuna Gwamna El-Rufa’i ba zai iya daukar zafin adawar siyasa ba.
“A watanni baya Gwamna El-Rufa’i ya sa an shafa wa wani gida nawa fanti domin rusawa a garin Hunkuyi amma mazauna garin suka hana a rusa. Sai ga shi yau shi da kansa ya jagoranci sojoji a mota sun je sun rusa gidana da ke Lamba 11B, Titin Sambo a Kaduna. Wannan mataki ya nuna Gwamnan ba zai iya daukar zafin siyasa ba kuma wani mataki ne da ba zai yi wa Jihar Kaduna kyau ba,” inji shi.
Sannan a ganawarsa da manema labarai a ranar Talata, Sanata Hunkuyi ya ce ya yafe Gwamna El-Rufa’i kan lamarin, sai dai ya ce yana da wani gida idan Gwamnan yana son ya rushe shi.
“Ina son fadin wasu ’yan kalamai, ba ina nan ne don batun rushe min gida ba, ina nan ne don in nuna damuwa kan yadda ake amfani da karfi a karkashin dimokuradiyyar da mua sha wahalar kafuwarta,” inji shi.
Ya ce “Kuma ina son sanar da Nasir El-Rufa’i cewa ina da wani gidan da na taba ba shi, kuma ya kwana a ciki na wasu lokuta a lokacin da yake kawo muttane daban-daban don su zabe shi a matsayin Gwamna da ke kan titin kueen Elizabeth a Zariya. Ta yiwu ya manta kuma ta yiwu yana son ya kwace shi. Iyakar abin da zan fada ke nan.”
Dalilinmu na rushe gidan – KASUPDA
Hukumar KASUPDA wanda aka ce ita ta rusa gidan ta fitar da sanarwa inda ta ce an dauki matakin ne saboda Sanatan ya ki biyan kudin kasa tun shekarar 2010.
Sanarwar dauke da sa hannun Darakta Janar na Hukumar Kula da Filaye (KADGIS) Ibrahim Hussaini ya ce Hukumar KASUPDA tana kokarin kawar da gidajen da aka yi su ba bisa ka’ida ba ne.
Mun goyi bayan rushe gidan – APC
Kakakin Jam’iyyar APC bangaren Gwamna Salisu Tanko Wosono ya ce sun gamsu da matakin da gwamnatin jihar ta dauka na rusa gidan da aka mayar sakatariyar bangaren APC. Ya ce babu wata gwamnati da za ta tsaya wadansu mutane tsirari su nemi ta da fitina a jam’iyyar kamar yadda Sanata Suleiman ke yi.
Ya shaida wa Aminiya hakan ne a zantawarsu ta tarho a Kaduna, inda ya ce: “Hukuma ta ba da dalilanta na daukar wannan mataki a kan gidan Sanata Hunkuyi ta ce bai biya kudin kasa ba tun shekarar 2010 haka kuma a takardar da aka ba shi na gina gida ne ba na ofishi ba. Babu dokar da ta ce ka canja abin da ka nema za ka yi da filinka don haka an ba shi takardar yin gida ne kuma ya je ya bude ofishi. Don haka a matsayinmu na jam’iyya mun gamsu da matakin da hukumar ta dauka a kan gidan.”
Game da me ya sa sai da aka samu sabani a tsakanin Sanata Hunkuyi da Gwamna El-Rufa’i sannan aka fahimci bai biya kudin kasa ba, Wosono ya ce “Sanata Hunkuyi ya nemi raba jam’iyya gida biyu ne kuma ya mayar da gidansa ofishin jam’iyya. Sanannen cewa laifi ne babba ka raba jam’iyya gida biyu kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin jam’iyyarmu. Baya ga haka ai ba shi kadai ke sukar gwamnatin Malam El-Rufa’i ba akwai Sanata Shehu Sani. Wannan gwamnati ita ta yi musu riga da wando amma suke sukarta. Sannan ai akwai ’yan PDP an taba masu gida ne? Matakin kawai shi ne rashin bin doka da kin biyan kudin kasa kamar yadda hukumar ta fadi.”
Ya ce “A kullum abin da muke cewa shi ne a kalli inda muka fito da inda muke yanzu da kuma inda za mu je. Babu yadda za a yi a ce babu doka a kasa. Duk kasar da aka ce babu doka al’ummarta za ta kasance a cikin wani hali.”
Ya yi kira ga ’ya’yan Jam’iyyar APC su yi hakuri abin da ke faruwa, inda ya ce alkawarin da gwamnatin Malam El-Rufa’i ta dauka ne a gabanta don haka da yardar Allah Gwamnan zai cika musu alkawarin da ya yi masu na inganta rayuwarsu.
“Sanata Sule da ke cewa ba a cika masa alkawari ba, ya fito fili ya fadi alkawarin da ba a cika masa ba domin mun sani cewa alkawaran da Gwamna ya dauka ga al’ummar jiha ne a gabansa. Kuma muna da yakini jama’ar jihar za su sake ba shi dama a zaben badi domin ya kammala ayyukan alherin da ya soma,” inji shi.
Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin danladi Wada ya ci tura domin wayarsa a rufe take tun daga lokacin da aka rusa ofishin.
Cutar dimuwa ce ta kama gwamnatin -PDP
Ibrahim Wosono shi ne Sakataren Jam’iyar PDP a jahar Kaduna ya kuma bayyana ra’ayinsu a kan dambarwar siyasar da ke faruwa cikin APC a jahar Kaduna, inda ya ce a matsayinsu na ‘yan PDP tuni sun ga alamomi da za su ba su damar kwace mulki a hannun APC a jahar Kaduna.
A cewarsa, babu ruwansu da rikici da ke tsakanin Sanata Suleiman Hunkuyi da kuma gwamatin jahar, amma abin damuwa kawai shi ne idan har dan jam’iyyar APC zai yi magana kuma gwamnatin jam’iyyarasu ta dauki irin wannan mataki a kan dan jam’iyyarta to ina kuma ga ’yan PDP idan sun fara magana? “ Mu tuni mun ga alamu da za su sa mu karbi mulki a hannun wannan gwamnati ta APC a jahar Kaduna tun kafin wannan rikici nasu ya yi nisa. Abin da na sani shi ne ita gwamnati hakkinta ne ta samar da tsaro ga jama’ar jahar ,amma tunda wannan gwamnati ta hau abin sai tabarbarewa yake a jahar.’’
“ Babu zaman lafiya a Kaduna, misali, dubi abin da ke faruwa a Birnin gwari da Kudanci jahar, duk babu zaman lafiya,”yan siyasa sace su ake yi, manoma yanzu tsoron zuwa gonakinsu suke yi domin tsoron kada a sace su.’’
“ Babu aikin yi, duk da alkawarin samar da aikin yi, yanzu wannan gwamnati ta El-Rufa’i ta kori ma’aikata sama da dubu 44 a jahar. Babu wani abu na cigaba a wannan jaha tun da ya hau mulki. Duk kuwa da makudan kudaden da ya samu. Muna da bayanan kudin da aka samu amma baba aikin da za ka nuna ka ce an yi ko an kammala.’’
“ Saboda haka rikicinsu da Sanata Hunkuyi harka ce tasu ta cikin gida, babu ruwanmu, amma abin tsoron shi ne idan za su dauki mataki a kan dan uwansu da ya nemi kila su gyara wani abu da suke yi ba daidai ba, me zai faru idan ‘yan adawa ko PDP sun fito sun fara magana?’’
“ Mu muna ganin ko shakka babu cutar dimowa da hauka ce ta kama gwamnatin jahar Kaduna tunda yanzu ga shi suna takura kansu da kansu,” inji shi.
Majalisar Dattawa ta yi Allah wadai da rushe gidan:
Sanata Shehu Sani ya jawo hankalin Majalisar Dattawa game da rushe gidan ba tare da sanarwa ba, inda ya tunatar da majalisar cewa shekara daya ke nan da Gwamnan ya rushe gidan Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Arewa maso Yamma.
Mataimakin Shugaban Majlisar Dattawa Sanata Ike Ikweremmadu wanda ya jagoranci zaman majalisar ya ce: “Dimokuradiyya ba ta zuwa da irin wannan zalunci da mulkin Gadara. Na yi Allah wadai da wannan aika-aika kuma ina fata ba za a sake irin haka ba. Bai kamata a rika wuce gona da iri a fagen mulki ba, kada a kure hakurin mutane. Kuma ina jaje ga Sanatan da ya rasa gidansa.”
Tinubu zai yi nasarar dinke baraka – Sakataren APC na kasa
Babban Sakataren APC na kasa, Alhaji Maimala Buni, ya bayyana cewa suna da kyakkawan zato cewa Sanata Bola Tinubu zai dinke barakar da ke addabar jam’iyar su.
Maimala Buni dai ya bayyana haka ne jim kadan bayan sanarwar da shugaba Buhari yayi na dora nauyin sasanta ‘yan jam’iyyar a kan Tinubu. “Ai babu wata matsala da ba ta da mafita in dai an yi abin da ya dace. Shugaba Buhari ya dauki matakin da ya dace; shi kuma jagora Tinubu ba kanwar lasa ba ne a hidimar siyasa. In sha Allahu zai yi nasara a wannan nauyi da aka dora masa.”
“Tabbas jam’iyyar mu ta APC za ta tsallake wannan tafki na matsaloli har kuma ta shiga zabe mai zuwa da karfinta,” inji shi.