✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rundunar ’yan sandar Jihar Katsina ta gargadi ’yan siyasa

A jiya Alhamis ce Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina a karkashin jagorancin Kwamishina Sanusi Buba ta gargadi ’yan siyasa da masu ruwa- da-tsaki da sauran jama’a…

A jiya Alhamis ce Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina a karkashin jagorancin Kwamishina Sanusi Buba ta gargadi ’yan siyasa da masu ruwa- da-tsaki da sauran jama’a su kiyaye dokokin da aka gindaya da suka hada da takaita zirga-zirga da sauransu a lokacin zaben gobe.

Kwamishinan ya ce, rundunarsa ta tanadi duk wasu matakai na ganin cewa an aiwatar da zaben Gwamna da na Majalisar Dokoki a gobe Asabar cikin kwanciyar hankali da lumana.

Kwamishinan ya ce an yi dokar takaita zirga-zirgar ababen hawan da ba su cikin masu aikin zabe, kuma an hana tafiya a tsakanin iyakoki ba wai na kan iyakar kasa ba hatta a tsakanin jiha da jiha da makamantan haka.  Sannan ya yi kira ga iyaye su kula da ’ya’yasu don gudun tayar da wata fitina a lokacin zaben, inda Kwamishinan ya ce babu sani ba sabo ga duk wanda aka kama ya karya dokar da aka kafa.