✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rundunar ’yan sandan Gombe ta ba iyalan jami’anta da suka mutu N18m 

Rundunar ta ba iyalai 25 tallafin miliyan 18

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe, Oqua Etim, ya mika wa iyalan jami’an rundunar su 25 da suka rasu a bakin aiki cakin kudi Naira miliyan 18 da dubu 500.

Kwamishinan ya ce wannan kudi wani tallafi ne daga Babban Sifeton Yan Sandan Najeriya, Alkali Baba Usman da kuma Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sanda don rage musu radadin mutuwar iyalai da iyayensu.

A cewarsa, yanzu an zo lokacin da magadan mamatan za su gane cewa iyayensu sun hidimta wa kasa ta hanyar aiki da hukumar da za ta share musu hawaye.

Daga nan sai ya yi kira gare su da su yi amfani da kudin ta hanyar da ta dace domin su amfane su.

Wasu iyalan jami’an da suka rasu da suka zanta da Aminiya cikin alhini, Atiku Ibrahim da Ruth Yusuf, sun nuna farin cikin su ga tallafin domin a cewar su, hakkokin ’yan uwansu da suke tsammani an riga an biya su, shi kuma wannan wani tallafi ne da basu san da shi ba.

Sun kuma kara gode wa hukumar da Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar bisa wannan tagomashin.