✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rundunar Tsaron Farin Kaya ta girke jami’anta a Sansanonin Gudun Hijira a Bama

Rundunar Tsaron Najeriya ta Farin Kaya (NSCDC) ya bayar da sanarwar girke jami’anta 1,500 a Bama na Jihar Borno, don kara inganta tsaro da kuma…

Rundunar Tsaron Najeriya ta Farin Kaya (NSCDC) ya bayar da sanarwar girke jami’anta 1,500 a Bama na Jihar Borno, don kara inganta tsaro da kuma kula da jigilar maida ‘yan gudun hijirar da Boko Haram ta raba da muhallan su.

Hukumar ta ce ta dauki wannan mataki ne bisa umarnin da Gwamnatin Tarayya na cewa Sojoji da ‘yan sanda da kuma jami’an farin kaya su aike jami’ai 1,500 kowannen su zuwa yankin don tabbatar da tsaro sannan da kuma bai wa ‘yan gudun hijirar kwarin gwiwa don sake gina muhallansu.

Babban Kwamandan Rundunar ta (NSCDC), Abdullahi Muhammadu Gana, wanda ya bayyana haka a karshen wannan watan, inda ya kara da cewa hukumar ta shirya rundunar musamman mai suna ‘Special Bama Skuad’ (SBS) don ci gaba da daidaita harkokin tsaro a yankin da kewaye.

A yayin da yake jawabi ga tawagar mahukuntan da Kwamandojin Sashe da na jihohi, Gana ya bayyana cewa babban makasudin wannan tsari na rundunar (NSCDC) wacce za ta kasance cikin garin Bama don karbar ‘yan gudun hijirar da za su dawo, haka kuma za su samu horo na musamman gabanin isar sub akin aiki.