✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rundunar Sojojin Sama za ta fara kera jirage a Najeriya

Rundunar Sojin Saman ta ce kamfanin zai zama mafi girma a Afirka.

Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya ta ce za ta kafa kamfanin kera jiragen sama a Osogbo, babban birnin Jihar a jihar Osun.

Air Marshal Oladayo Amao, Babban Hafsan Sojin Sama ke ya bayyana haka yayin bikin mika aikin da gwamnatin Osun ta yi ga na titin jirgin sama ga rundunar a jihar.

Amao, wanda AVM M.O Onilede ya wakilta a wajen taron, ya ce rundunar sojin a wani bangare na yarjejeniyar da aka cim ma da gwamnatin kan karbe filin jirgin saman jihar, tuni ta mayar da cibiyar bincike da raya kasa daga Kaduna zuwa Osogbo.

Ya ce rundunar za ta kuma samar da ‘Birnin Jiragen Sama’ a Osun, inda kuma ya ce tuni tattaunawa ta yi nisa da abokan hulda daga kasashen waje kuma za a fara aikin da zarar an cim ma yarjejeniya.

Amao ya ce birnin sufurin jiragen saman zai kasance irinsa na farko a nahiyar Afirka.

“Aikin a jihar zai kuma hada da masana’antar kera jiragen sama da gyaransu da kuma kafa cibiyar kera motoci marasa matuka, da dai sauransu,” inji shi.

Amao ya ce sojojin saman za su bunkasa titin jirgin saman na Osun saboda ya kasance “muhimmin wuri don ayyukan sojojin sama da kuma taimaka wa jiragen kasuwanci.”

“Za mu inganta titin jirgin sama; za mu gina hanyoyi guda biyu.

“Maimakon mutane su rika tafiya Akure, Ibadan ko Legas don yin jigila, da zarar an kammala titin jirgin saman, za su iya amfani da shi,” inji shi.

A nasa jawabin, Gwamna Jihar, Gboyega Oyetola, ya gode wa rundunar saboda kawo aikin jihar, inda ya ce an gina filin sauka da tashin jiragen sama na Ido-Osun a 1936, kuma dakarun sa-kai na Afirka na lokacin ne suka yi amfani da shi a lokacin Yakin Duniya na Biyu.

Oyetola ya ce Gwamnatin Tarayya ta bai wa jihar dama ta fara inganta filin jirgin sama bisa rokon da jihar ta yi tare da fatan gina shi zai kara habaka tattalin arzikin jihar.