✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rundunar sojin sama ta tura jiragen yaki zuwa Jos

Rahotanni na nuna cewa rundunar sojin saman Najeriya ta tura jiragen yaki zuwa garin Jos, babban birnin Jihar Filato domin kawo karshen tashe-tashen hankula da…

Rahotanni na nuna cewa rundunar sojin saman Najeriya ta tura jiragen yaki zuwa garin Jos, babban birnin Jihar Filato domin kawo karshen tashe-tashen hankula da jihar ke fuskanta.

Sanarwa ta fito ne daga  hedkwatar rundunar, inda ta ce babban hafsan sojin saman Najeriya, Air Marshal Siddique Abubakar ne ya bayar da umarnin tura jiragen yakin bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya yi umarni da a dakile tashe-tashen hankula da ake same a jihar kamar yadda BBC ta ruwaito.

Rundunar sojin saman ta tura jirgin sama samfurin L-39ZA da kuma jirgi mai saukar angulu samfurin EC-135, wadanda za su bayar da kariya ga rundunar da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Wannan dai ba shi ne lokaci na farko da rundunar sojin saman Najeriya za ta tura jiragen yaki wani bangare na kasar domin tallafa wajen tabbatar da zaman lafiya ba.

Umarnin nan ya zo ne sakamakon tashe-tashen hankulan da ke sake kunno kai a baya-bayan nan, inda aka kashe a kalla mutum 35 aka kuma jikkata wasu da dama a hare-haren da aka kai  a wasu kauyuka a karamar hukumar Bassa a jihar.