Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Manjo Janar Farouk Yahaya, ya amince da nadin Birgediya Janar Onyema Nwachukwu a matsayin Daraktan Hulda da Jama’a na rundunar.
Wata babbar majiyar soja ta shaida wa Aminiya ce nadin ya fara aiki ne nan take.
Nwachukwu Zai karbi mukamin ne daga hannun Mohammed Yerima wanda ya fara aikin a watan Fabrairun bana bayan da aka nada marigayi Laftanal Janal Ibrahim Attahiru a matsayin Babban Hafsan Sojin Kasa a watan Janairu.
Kazalika, rundunar ta kuma sanar da sauya wa Janar-janar 11 da ma wadansu manyan jami’an sojan wuraren aiki a wani gagarumin garambuwal da take yi.
Sauya wuraren aikin na zuwa ne kwanaki kadan bayan rahotanni sun yi zargin cewa za a yi wa manyan sojoji har guda 29 da suka zarce Babban Hafsan Sojin na yanzu, ritayar dole.
Wata sanarwa da Daraktan Watsa Labarai na rundunar mai barin gado, Mohammed Yerima, ya fitar a daren Juma’a ta ce an yi wa manyan jami’an rundunar sauye-sauyen wurin aiki ne domin cika burin Babban Hafsan wajen “Samar da sojin Najeriya da ke shirye domin sauke nauyin da aka dora masa game da tsaron kasar.”