Kimanin sa’o’i 72 bayan rasuwar Babban Hafsan Sojojin Kasa na Najeriya, Laftanar-Janar Ibrahim Attahiru, hankula sun fara karakata wurin wanda zai dare mukamin mafi girma a Rundunar.
Mutum 11 ciki ne har da Janar Attahiru suka mutu ranar Juma’a a hatsarin jirgin sojin sama mai suna Beachcraft 350 a Kaduna, aka kuma yi musu jana’iza ranar Asabar a Abuja cikin jimami da zubar kwalla.
- An kori hadimin Dan Majalisa saboda Shekau
- Mahara sun kashe 3, sun tashi kauyuka 8 a Sakkwato
- An kashe mutum shida ’yan gida daya a Filato
Masana harkokin tsaro da muka gana da su ranar Lahadi sun ce ya zama dole a yi gaggawar nada magajin Janar Attahiru domin ci gaba da bai wa sojojin da ke bakin daga a yaki da ta’addanci a yankin Arewa-maso-Gabas karsashi.
Wani jami’i kuma ya jaddada cewa a yanzu ya zama dole a nemi magajin Janar Attahiru domin dorawa daga nasarorin da marigayin ya cimma kan Boko Haram a dan karamin lokacin da ya yi a matsayin Babban Hafsan Sojin Kasa.
Ya zuwa daren Litinin, an fara rade-radi kan sunayen wasu manyan hafsoshin soja wadanda daga cikinsu za a zabi wanda zai zama sabon Babban Hafsan Sojin Kasa, a daya hannun kuma ake ta kamun kafar masu fada a ji a Abuja.
Wadanda aka fi tsammatawa mukamin su ne Manjo Janar Danjuma Ali-Keffi da Manjo Janar Biliyaminu Ahanotu da Manjo Janar Jamil Sarham da Manjo Janar Faruk Yahaya.
Tun a ranar Asabar da dare aka fara yada jita-jita cewa Ali-Keffi ya zama sabon Babban Hafsan Sojan Kasan.
Kwanakin baya ne aka nada Manjo Janar Alin a matsayin Babban Jami’in Soja (GOC) na Runduna ta 1 da ke Kaduna.
An ce yana da kusanci da Fadar Shugaban Kasa inda a bara aka ba shi jagorancin sashin bankado bayanan asiri na rundunar sojin, wanda ya kai ga kame mutanen da ake zargin masu bayar da tallafin kudi ga ’yan ta’adda a fadin Najeriya.
Manjo Janar Ahanotu, wanda Shugaban bangaren tsare-tsare da manufofi a rundunar sojin, shi ne jami’i na na biyu mafi girman mukami a rundunar.
Ana jinjina wa rawar da ya taka a jagorancin kama Shugaban Boko Haram na farko, Mohammed Yusuf a 2009.
Sauran wadanda ake tunanin za su samu mukamin su ne Kwamandan Rundunar Hadin Gwiwar Kasashen Yankin Tafkin Chdai (MNJTF), Manjo Janar Jide Jeleel Ogunlade sai kuma Babban Kwamandan Operation Hadin Kai, mai yaki da Boko Haram, Manjo Janar Faruk Yahaya.
Manjo Janar Sarham, tsohon Kwamandan Kwalejin NDA, kwanan nan aka nada shi a mukamin GOC na Runduna ta 82 da ke Fatakwal, Jihar Ribas.
Yi watsi da kabilanci, masanin tsaro ya bukaci Buhari
A wata ganawa ta wayar tarho, masanin tsaro, Kabiru Adamu, ya nuna bukatar Shugaban Kasa ya yi watsi da batun kabilanci, ya yi amfani da girman mukami da kwarewar jami’in soja a fagen daga kafin ya nada kowa a mukamin.
Ya ce dama ce ga Shugaban da ya wanke kansa a wajen wadanda suke cewa yana nuna wariya ga al’ummar Kudu-maso-Gabas ta hanyar nada wani daga yankin, wanda hakan zai lafar da koke-kokensu.
“Batun daidaito yana da matukar muhimmanci; cancanta ma tana da matukar muhimmanci.
“Najeriya na cikin kalubale sosai a yanzu; wasu za su ce muna cikin yaki.
“Idan muna cikin yaki ne, to kuwa muna bukatar shugaban sojan da zai kawo mana nasara a yakin da muke fama da shi.”