Rundunar Sojin Ruwa da ke Ibaka, a Karamar Hukumar Mbo a Jihar Akwa Ibom ta kama mutum 20 dauke da buhun shinkafa ’yar waje 1,425 da ake zargin an shigo da ita ce ta barauniyar hanya, inda masu fasakwaurin suka yi amfani da jiragen kwalekwale hudu don shigowa da ita.
Kwamandan Sojin Ruwan Kyaftin Peter Yelmi wanda ya wakilci babbban jami’i mai kula da ayyukan yau da kullum na hukumar hana fasakwauri, ya ce jami’ansa masu sintiri a kan ruwa ne suka kama wadanda ake zargin.
Kyaftin Peter Yilme ya ce masu fasakwaurin sun yi amfani da kwalekwale kanana wajen safarar shinkafar daga kasar Kamaru suka shigo da ita. Ya ce ko a watan jiya sai da suka kama buhun shinkafa 3,800 da duro 60 na man gas da aka sarrafa shi ta hanyar amfani da fasahar cikin gida.
Daya daga cikin wadanda aka kama mai suna Effion Okon, ya shaida wa wakilinmu cewa “Tsautsayi ne wannan ne karo na farko da ya taba yin wannan harka ta shigo da shinkafa daga kasar Kamaru kuma Naira 2,000 yake biya kudin fito idan har aka kawo masa ita gida.”
Ya ce buhu 200 ya dauko cikin kwalekwalen ga shi kuma ba a yi dace ba an kama su.
An mika wadanda ake zargin ga Hukumar Kwastam da ke Jihar Akwa Ibom domin daukar mataki na gaba.