A ranar 4 ga watan Oktoba ne, Babban Hafsan Sojan kasa Laftanar Janar Tukur Buratai ya kaddamar da sabon ofis da zai rika lura da koke-koken cin zarafin da ake zargin sojoji da aikatawa a Maiduguri.
Ofishin dai yana Barikin Brigediya Janar Maimalari ne inda hedkwatar samar da zaman lafiya dole yake. Rundunar sojan a watan Fabrairun bara, ta sanar da cewa ta bude fannin da zai rika lura da matsalolin cin zarafin mutane a hedkwata, inda za a rika amsa koke-koken mutane kan cin zarafin da sojojin ke yi a lokacin aikinsu. An yanke shawarar bude wannan ofishin ne bayan an ta samun koke-koken cewa sojoji suna cin zarafin mutane a lokacin da suke yaki da Boko Haram. Ana sa ran ofishin zai yi aiki da tsarin dokokin ayyukan wadanda suke yaki da kungiyar Boko Haram a yankin Arewa Maso Gabas.