Rukunin farko na maniyyata Aikin Hajjin bana su 544 sun tashi daga filin jirgin saman kasa da kasa da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno zuwa kasar Saudiyya don sauke farali.
Jirgin dai na kamfanin Max Air, shi ne na farko da ya tashi yayin da aka kaddamar da jigilar maniyyatan domin gudanar da Aikin Hajjin na shekarar 2022, wanda aka fara ranar Alhamis.
- Zargin batanci: An fara sauraron kaset din wa’azin Abduljabbar a kotu
- ‘Tinubu ya yi wa Gwamnonin APC alkawarin Mataimakin Shugaban Kasa’
Da yake jawabi yayin kaddamar da tashin alhazan, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci maniyyatan da su zama jakadun Najeriya a kasa mai tsarkin.
Shugaban, wanda Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya wakilta, ya ce, “Aikin Hajji ibada ce da ke da matukar wahala, wacce kuma take bukatar hakuri, juriya, da’a da kuma sadaukarwa.
“Ina kira gareku da ku kiyaye dukkan matakan kariyar cutar COVID-19, don kare kanku da ma sauran mutane iya zamansu a aksa mai tsarki.”
Buhari ya ce dawowar jigilar ’yar manuniya ce kan irin kokarin Gwamnatin Tarayya wajen dawowar zaman lafiya a Jihar ta Borno.
Shugaban ya kuma yi kira ga Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) da duk masu ruwa da tsaki da su tabbatar da yin duk abin da ya dace wajen samun nasarar shirin a bana.