Mutane 10 ne ake fargabar sun mutu sakamakon ruftawar wani bene a safiyar ranar Alhamis a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.
Babban Manajan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Oyo, Mista Yemi Akinyinka ne ya tabbatar da hakan yayin ganawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN).
- Ya kamata a koma koyarwa cikin harsunan Nijeriya — Masana
- Tsadar fetur: Dangote da ’yan kasuwa sun sake sa zare
Akinyinka ya ƙara da cewa wasu mutum bakwai sun samu raunuka a ruftawar ginin wanda rahotanni suka ce ya faru da misalin ƙarfe 2:00 na tsakar dare a unguwar Jegede Olunloyo da ke Ibadan a ranar Alhamis.
Ya ce, Hukumar ta samu kira mai cike da damuwa game da ruftawar ginin da misalin ƙarfe 2:00 na tsakar daren inda nan take ta tura jami’ai zuwa wurin.
“Hukumar kashe gobara ta jihar Oyo ta samu kiran waya da misalin ƙarfe 2 na dare, a unguwar Jegede Olunloyo, a Ibadan inda aka ciro mutane 10 daga cikin baraguzan benen da ya ruguje, yayin da aka ceto mutane bakwai da ransu,” in ji shi.
A cewar babban manajan, ana ci gaba da aikin ceto waɗanda ake zargin sun maƙale a ƙarƙashin baraguzan ginin.