A ranar 28 ga watan Agustan da ya gabata ce, yau kwanaki 44, daidai gwamnatin tarayya ta ba da umurnin a rufe dukkan kan iyakokin kasar nan, musamman na kasa, bayan ta kafa wani karfaffan Kwamiti na kasa baki daya da ya kunshi jami`an Hukumar Hana Fasa Kwauri wato Kwastam da na Hukumar Kula da Shigi da Fici wato Imigireshen da `yan sanda da na sojojin sama da na kasa da na ruwa da jami`an tsaro na farin kaya wato DSS da dai sauransu. Makasudin kafa wannan Kwamiti na daya baki daya kamar yadda gwamnatin tarayyar ta sanar bai wuce wasu dalilai kamar haka ba:- Na daya a hana shigo da kayayyakin da aka haramta shigo da su irin su shinkafa da man girki kwata-kwata. Da kuma hana shigo da motoci ko wadanne iri ta haryar fasa kwauri, sai dai ta tashoshin jiragen ruwan kasar nan, ta yadda za a iya biyan gwamnatin kudin fito.
Sai kuma batun hana shigo da muggan makamai irin su bindigogi da harsasai da makamantansu, kai har da hana shigowar haramtattun bakin haure daga kasashen makwabtanmu, da yadda za a kara samun kudaden shiga. Hanzarin da gwamnatin tarayyar ta bayar shi ne, ta wannan hanya ce ake ta samun yawaitar tashe-tashen hankula irin na `yan kungiyar Boko Haram da `Yan bindiga dadi da yawaitar fashi da makami, matsalolin da ake ta fama da su a sassa daban-daban na kasar nan.
Daga fara wannan gagarumin aiki, zuwa ranar Juma`ar makon jiya, an ruwaito Kakakin Hukumar hana fasa kwauri na kasa kuma shuganan Kwamitin wayar da kan jama`a, musamman masu ruwa da tsaki a kan rufe kan iyakokin wato Mukaddashin Kwanturola Mista Joseph Attah a cikin shirin BARKA DA HANTSI na gidan Radiyo Freedom da ke Kano yana cewa zuwa wancan lokaci an yi nasarar kama mutane 146, da suka yi kokarin shigo cikin kasar nan ba tare da izini ba, da kuma buhunnan shinkafa sama da dubu 19, da buhunnan takin zamani samfurin NPK 131, da ya yi zargin masu tada kayar baya suna amfani da shi wajen hada bama-baman da sukan kai hare-hare da su, da tankunan man fetur biyu, da jarkoki dubu 5.
Mukaddashin Kwanturolan ya ce ko kusa gwamnatin tarayya ba ta da aniyyar kuntata wa `yan kasa bisa ga rufe kan iyakokinnan da ta yi na wani dan lokacin da bai fadi wa`adinsa ba, illa dai don ta kare dukkan matakan ganin habakar tattalin arziki da na tsaron kasar nan da mutanenta.
Ya jawo hankalin `yan kasa a kan irin yadda duk shekara ake fitar da makudan kudaden kasashen waje daga kasar nan, don sayo shinkafa ko man girki da sauran makamantan kayayyakin abinci da abin sha da ma tsinken sakace da muke iya samarwa, ya ce ba abin da yake haifarwa sai bunkasa tattalin arzikin wadancan kasashe, mu kuma muna kara durkusar da kanmu da kanmu ta hanyoyi daban-daban, wasu kayayyakin ma irin su shinkafa da man girki akasari amfaninsu ya kare in ji Mista Attah.
A cikin tattaunawar ta shirin na BARKA DA HANTSI Alhaji Dalhatu Abubakar shugaban Cibiyar `yan kasuwa, masana`antu, ma`adanai da Ayyukan gona reshen Jihar Kano kuma mai kamfanin sarrafa shinkafa a Kanon, cewa ya yi suna maraba da wannan hani na rufe kan iyakokin kasar nan da kuma damarar da gwamnatin ta daura ta hana shigo da shinkafa da duk wasu nau’in kayayyakin da kasar take iya samarwa. Yana mai ba da tabbacin cewa hakan zai sa a kara samun manoma a kasar nan da za su kara dukufa wajen noman shinkafar, su kuma masu masana`antun sarrafa shinkafa suna ba manoman shinkafar kasar nan tabbacin za su saye dukkan shinkafar da suka noma.
Shi ma Alhaji Auwalu Mariri, wani dan kasuwar shinkafa a babbar kasuwar kayayyakin masarufi ta Kwanar Singa da ke Kano, cewa ya yi suma suna maraba da wannan aniya ta gwamnatin tarayya. Yana mai cewa “Mu da ma alatilas, ba bisa son ranmu ba, sai don bisa ga bukatar `yan kasa masu son lallai sai sun ci shinkafar kasashen waje ya sa muke yin fataucinta.” Wani batu da Alhaji Auwalu ya ce babban abin jin dadi ga su `yan kasuwar da su ke fataucin shigo da shinkafar kasashen waje yanzu, shi ne irin yadda suke da kwanciyar hankali da kuma rashin zullumin asarar da kan same su, shi ne, a da duk inda suka dauko ko za su kai shinkafar kasashen waje, a koda yaushe cikin zullumi da fargaba suke na shinkafar ko za ta isa inda za su kai ta lafiya, ba tare da jami`an Kwastam sun kama ta ba, abinda ya ce yanzu wannan ya zama tarihi, kuma `yan kasa sun dawo sun rungumi cin shikafar gidan.
Tun a ranar 15 ga watan Nuwambar 2015, bayan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta zo kan karagar ta kaddamar da shirin bunkasa noman shinkafa da Alkama a Jihar Kebbi, ta hanyar bayar da rancen biliyoyin Naira ga Manoman jihar a karkashin Babban Bankin kasa, tare da shan alwashin zuwa 2018, za ta hana shigo da shinkafa daga kasashen waje dungurum-gum. Tun daga wancan lokaci Babban Bankin duk shekara yake kara fadada shirin da karin biliyoyin Naira, zuwa sauran jihohin kasar nan da suke iya noma shinkafa. Su kuma `yan kasuwa suke ta kakkafa da fadada masana`antun sarrafa shinkafa.
Sai dai kash! Abin ka da mutanen kasar nan, ba sa mayar da kudaden gwamnati in an ba su rance tamfar sun samu nasu kason, wajen yin kememe su ki biya. Alal misali a Jihar Kano da aka fara kaddamar da shirin yau shekara uku, an ba namoman shinkafa bashin Naira biliyan 10, amma zuwa yanzu da kyar manoman suka biya Naira miliyan 100, wato kashi 1 cikin 100, na yawan kudin kamar yadda shugaban kungiyar masu noman shinkafa wato RIFAN ta kasa reshen Jihar Kano Alhaji Abubakar Haruna ABH, ya shaida wa shirin na BARKA DA HANTSI. Da irin wannan mugun hali ina za a kai ga nasarar da ake bukata?
Idan ba so muke mu dawwama a matsayin bayin kasashe irin su Indiya da Tailand, da muke shigo da shinkafa daga kasashen su ba to ya kamata duk wanda aka ba irin wancan bashi da ake son ya biya cikin noma uku ya rika biya don amfanin wasu. Ita kuma gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi akwai bukatar su ci gaba da ba ko na da dukkan irin tallafin da ya kamata walau bashin ne kayyakin noman ne ko kudade ga manoman kasar nan akan kari.
Su kuma masu Masana`antu sarrafa shinkafar su tabbatar da suna sayen dukkan shinkafar da aka noma akan farashi mai inganci rani da damina. Da yardarm Allah wannan hanin shigo da shinkafa kasar nan zai dore. Saura kuma na hana shigo da yadudduka a duk lokacin da aka farfado da Masakun kasar nan. Tun samun `yancin kai yau shekara kusan 60, wannan jajircewar mu ka rasa.