✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rufa-rufa Emefiele ya yi wa Buhari kan sauya kudi —Doguwa

Doguwa ya nuna shakku kan halascin shugabancin CBN a karkashin Emefiele, wanda dan siyasa ne

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya zargi Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele da yi wa Buhari rufa-rufa kan sauya fasalin takardun Naira 200, N500 da kuma N1,000.

Doguwa wanda dan Jam’iyyar APC ne, ya ce ya yi imanin Shugaba Buhari zai dauki matakan da suka dace don gyara barnar sauya kudin ya haifar.

“Shugaban Kasa a matsayinsa na babban jami’in gwamnati kuma shugaban sojojin Najeriya, na san dole zai yi abin da ya dace, amma Emefiele ya yaudare shi.

“Watakila lokacin da aka gabatar wa shugaban kasa batun sauyin kudin ba a fahimtar da shi irin halin da za a shiga ba, amma ina da yakinin zai bi hanyar da ta dace don yin gyara,” in ji shi.

A tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels a ranar Litinin, Doguwa ya ce sauya takardun kudin zai kawo cikas ga zabukan 2023.

Kazalika ya nuna shakku kan halascin shugabancin CBN a karkashin Emefiele, wanda ya nemi takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.

Jigon na jam’iyyar APC ya ce ya gana da shugaban kasar a ranar Lahadi, inda ya nuna rashin gamsuwarsa kan gazawar Gwamnan CBN wajen amsa goron gayyatar da majalisar ta aike masa.

Idan ba a manta ba sauya kudaden ya jefa ’yan Najeriya da dama cikin wahala, lamarin da ya sanya su bin dogayen layuka a bankuna don cirar sabbin kudaden.

Matakin ya haifar wa da shugaba Buhari suka daga talakawa, lamarin da ya kai wasu fusatattun matasa jifan ayarin motocinsa da jirginsa a yayin ziyarar aiki da ya kai jihohin Katsina da Kano a baya-bayan nan.

%d bloggers like this: