Shahararren dan kwallon kulob din Manchester United da ke Ingila Wayne Rooney a ranar Litinin da ta gabata ne ya ba magoya bayan kulob din hakuri a bisa jan katin (red card) da alkalin wasa ya ba shi a wasan da kulob din ya yi da na West Ham a gasar rukunin firimiya ta Ingila a ranar Lahadin da ta wuce.
“A gaskiya na ji takaicin jan katin da aka ba ni don haka nake mika sakon hakuri ga magpoya bayan kulob din United” kamar yadda kafar sadarwar BBC ta ruwaito a yanar gizonta.
Saboda jan katin da aka ba Rooney ba zai sake yi wa kulob din United wasa ba sai a ranar 2 ga watan Nuwamban wannan shkeara watau a ranar da kulob din zai kece raini da na Manchester City a gasar rukunin firmiya.
Kocin West Ham Sam Allardyce ya bayyana abin da Rooney ya aikata a wasan na rafke dan kwallonsa babu gaira babu dalili a kan rashin hankali kamar yadda shi ma Manajan kulob din Manchester United Louis ban Gaal ya amince da matakin da alkalin wasan ya dauka na ba dan kwallonsa jan kati a kan aikata ba daidai ba.
Rooney ya ba magoya bayan United hakuri
Shahararren dan kwallon kulob din Manchester United da ke Ingila Wayne Rooney a ranar Litinin da ta gabata ne ya ba magoya bayan kulob din…