✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rooney da Eto’o da Drogba za su zo Najeriya don karrama Yobo

Tsohon kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Joseph Yobo ya sanar da yin ritaya daga kwallon kafa a ranar Litinin da ta gabata…

Tsohon kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Joseph Yobo ya sanar da yin ritaya daga kwallon kafa a ranar Litinin da ta gabata a Legas.
Ya ce daga cikin shirye-shiryen yin ritayar tasa, cibiyarsa tare da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Ribas sun shirya bikin karrama shi inda ta shirya wasan kwallon kafa na sada zumunta inda ta gayyato wadansu daga cikin fitattun kwallon da za su fafata a wasan da zai gudana a Najeriya.
Kamar yadda dan kwallon ya sanar a lokacin da yake jawabi, ya ce cibiyarsa tare da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Ribas tuni suka mika sakon gayyata ga shahararrun ’yan kwallo irin su Wayne Rooney na kulob din Manchester United da ke Ingila da Didier Drogba da Samuel Eto’o da Yaya Toure na Manchester City da sauransu.  Sannan tsohon kocin Joseph Yobo a kulob din Eberton Dabid Moyes yana daga cikin ‘yan gayyatar.
dan kwallon ya ce ana sa ran a ranar 25 ga watan Mayun 2016 ne za a gudanar da wasan na sada zumunci a filin wasa na Adokie Amiesimaka da ke Fatakawal na Jihar Ribas.
Joseph Yobo wanda ya kafa tarihi a kungiyar Super Eagles a matsayin wanda ya fi dadewa yana yi wa kungiyar kwallo, ya fara yi wa kungiyar wasa ne tun a shekarar 2001.  Kenan, dan kwallon ya shafe kimanin shekara 13 a kungiyar kafin ya yi ritaya daga yi wa kungiyar kwallo.
Kafin ritayarsa ya yi wa Super Eagles wasanni fiye da 100 kuma ya halarci gasar cin kofin duniya daban-daban har sau uku sannan ya halarci gasar cin kofin Afirka sau shida.  Ya yi wa Super Eagles wasan karshe ne a gasar cin kofin Nahiyar Afirka a shekarar 2013.
Ya buga wa kulob da dama kwallo a Nahiyar Turai da suka hada da Standard Leige na Beljiyam da Marseille na Faransa da Eberton na Ingila da Fenerbahce na Turkiyya da kuma na Norwich City da ke Ingila kafin ya yi ritaya a ranar Litinin da ta wuce.