Bayan sanya hannu a kan kwantaraginsa da kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr da ke Saudiyya, Cristiano Ronaldo zai taimaka wa kasar a hankoronta na neman karbar bakuncin Gasar Cin Kofin Duniya da za a yi a 2030.
Fitaccen dan wasan dai ya kammala kokarin tafiya kungiyar ta Saudiyya ne ranar Juma’a gabanin bude kakar musayar ’yan wasa ta bana a watan Janairu.
- ’Yan Arewa ba su da wani dalilin kin zabar Tinubu — Ganduje
- Rashin kishi ne kiran gwamnati ta bude iyakoki – Masani
Dan wasan dai zai rika karbar Yuro miliyan 173 ne a kowacce shekara, ban da sauran kudadn alawus-alawus da zai rika karba.
An dai fara tattaunawar ce yayin Gasar Cin Kofin Duniyar da aka kammala a kasar Qatar, inda a karon farko zai bar Turai da buga wasan nasa.
Rahotanni sun ce dan wasan zai taimaka wa kasar wajen fafutukarta ta karbar bakuncin gasar a 2030.
Kasar wacce ke yankin Gabas ta Tsakiya dai zai za ta ta fafata da kasashen Masar da Girka wajen neman karbar bakuncin gasar nan da shekaru shida masu zuwa.