Kocin Kungiyar Kwallon Kafa ta Juventus, Massimiliano Allegri ya ce Cristiano Ronaldo zai ci gaba da zama a kungiyar sabanin rade radin da ake cewar zai sauya sheka zuwa wata kungiyar.
A wata ganawa da manema labarai kafin karawar da Juventus ta yi da Udinese, Allegri ya ce ya tattauna da tauraron dan wasan kuma ya tabbatar masa cewar zai ci gaba da zama a Turin.
- Sarakuna za su iya magance matsalar tsaro — Buratai
- Fulani sun fara tona asirin masu garkuwa da mutane a Taraba
Allegri ya ce Ronaldo na ci gaba da samun horo tare da takwarorin sa kuma ba ya fasa halartar shirye shiryen da suke na fara sabuwar kaka duk da rade radin da yake karantawa a jaridu.
Duk da rashin halartar wasan sada zumuntar da suka yi da matasan yan wasan Juventus ranar alhamis, mai horar da ’yan wasan ya ce Ronaldo na shirye domin yi wa kungiyar wasa a shekara ta 4 kuma ta karshe na kwangilar da ya sanya hannu akai.
Kalaman manajan na zuwa ne bayan da Ronaldo wanda ya zira kwallaye 29 bara ya fito fili ya yi watsi da zargin cewar yana shirin komawa Madrid.