✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronaldo ya yi barazanar barin kulob din Madrid

Shahararren dan kwallon kulob din Real Madrid Cristiano Ronaldo ya yi barazanar barin kulob din a karshen kakar wasa ta bana muddin mahukunta kulob din…

Shahararren dan kwallon kulob din Real Madrid Cristiano Ronaldo ya yi barazanar barin kulob din a karshen kakar wasa ta bana muddin mahukunta kulob din ba su yi masa karin albashin da zai yi daidai da na Lionel Messi na FC Barcelona da kuma na Neymar da ke kulob din PSG na Faransa ba.

Ronaldo wanda kawo yanzu ya zura kwallaye 15 a gasar zakarun kulob na Turai, tauraruwarsa na haskakawa ne musamman a yunkurin da yake yi na taimakawa kulob din Madrid wajen sake lashe kofin zakarun kulob na Turai a karo na uku a jere kuma sau 13 a jumilla.

A ranar Laraba mai zuwa ne kulob din Real Madrid zai yi wasa zagayen farko da kulob din Bayern Munich na Jamus a matakin semi fainal a gasar zakarun kulob na Turai kafin su sake haduwa a wasa zagaye na biyu kwanaki shida tsakani.

Ronaldo wanda ya fara kakar wasa ta bana da kafar hagu, kawo yanzu ya zura kwallaye 41 ne ga kulob din Madrid a dukkan wasannin da ya yi mata, kuma ana sa ran idan ya taimaki kulob din wajen sake lashe kofin zakarun kulob a karo na uku a jere zai iya zama Gwarzon dan kwallon duniya a karo na 6.

Rahotanni sun nuna kulob din Manchester United ne ya yi masa tayi mai gwabi a kokarin  dauke shi da hakan ta sa hankalinsa ya fara komawa Ingila don sake bugawa United kwallo.