✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronaldo ya samu kyautar Gwarzon dan kwallon Duniya a Dubai

A ranar Litinin da ta gabata ne aka zabi dan kwallon kulob din Real Madrid da ke sifen Cristiano Ronaldo a matsayin dan kwallon da…

A ranar Litinin da ta gabata ne aka zabi dan kwallon kulob din Real Madrid da ke sifen Cristiano Ronaldo a matsayin dan kwallon da ya fi kokari a shekarar 2014.  Wannan kamar wani gwaji ne na gasar Gwarzon dan kwallon duniya da Hukumar FIFA za ta gudanar a ranar 12 ga watan nan da muke ciki.
Zaben ya gudana ne a karkashin kulawar wata cibiya mai suna Globe Soccer Award da ke Dubai kuma ana hasashen akwai yiwuwar dan kwallon ya sake lashe Gasar Gwarzon dan kwallon Duniya da za a yi a ranar 12 ga watan nan da muke ciki.
Ronaldo dai ya samu wannan nasara ce bayan ya taimakawa kulob din Real Madrid na Sifen wajen lashe kofin zakarun kulob-kulob na Turai a karo na 10 da kuma kofin Sarki watau Kings Cup sannan shi ne ya kafa tarihin dan kwallon da ya fi zura kwallo a raga a gasar, bayan ya zura kwallaye 17 a raga.
Sai dai Ronaldo ya ce yana fata wannan kyauta da ya samu za ta share masa fagen lashe babbar kyauta ta Gwarzon dan kwallon duniya da za a yi a ranar 12 ga watan nan na Janairu.
Masana harkar kwallo da masu horarwa da ’yan jaridu ne suka gudanar da zaben.