✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronaldo ya sake zama Gwarzon dan kwallon Duniya a karo na 5

A ranar Litinin da ta gabata ne shahararren dan kwallon Fotugal da kulob din Real Madrid na Sifen ya sake zama Gwarzon dan kwallon Duniya…

A ranar Litinin da ta gabata ne shahararren dan kwallon Fotugal da kulob din Real Madrid na Sifen ya sake zama Gwarzon dan kwallon Duniya a karo na 5 a wani biki da Hukumar Shirya kwallon kafa ta Duniya (FIFA) ta shirya a Landan.

dan kwallon ya fafata ne da shahararrun ’yan kwallo uku da suka hada da Lionel Messi dan asalin Ajantina da kuma Neymar dan asalin Brazil.

Sannan a lokacin bikin ne aka zabi Kocin Real Madrid Zinedine Zidane a matsayin Gwarzon Koci a bangaren kwallon kafa na maza yayin da aka zabi Sarina Wigman a matsayin Gwarzuwar Kocin Mata ta bana.

Haka kuma Golan kulob din Jubentus na Italiya Buffon ne aka zaba a Matsayin Gwarzon Gola yayin da aka zabi dan kwallon gaba a kulob din Arsenal na Ingila Oliber Giroud a matsayin dan kwallon da ya fi zura kwallo mai kyau a raga (Pukas Award).

Shi dai Ronaldo ya sake samun nasarar lashe wannan gasa ce bayan ya taimaka wa kulob din Real Madrid na Sifen lashe kofunan La-Liga da kofin Zakarun Kulob na Turai (Champions League) a karo na biyu a jere da kuma taimaka wa kasar haihuwarsa Fotugal hayewa gasar cin kofin duniya.

Sannan a yayin bikin an zabi Gwarazan ’yan kwallo 11 daga kulob daban-daban da Hukumar FIFA ta karrama da suka hada da Crisitano Ronaldo da Lionel Messi da Buffon da Marcelo da Bonucci da Ramos da Albes da kuma Andre Iniesta.

Sauran sun hada da Modric da Koos da kuma Neymar.

Kococi da ’yan kwallo da kuma ’yan jarida ne suke gudanar da zaben a duk shekara.

Yanzu dai Ronaldo ya kamo Lionel Messi a yawan lashe wannan kyauta inda kowannensu yake da biyar-biyar a tarihin kyautar.