✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ronaldo ya lashe Kyautar Gwarzon Dan Wasan Karni

Ya yi wa sa’o’insa masu buga tamola zarra a tsakanin shekarar 2001 zuwa 2020

Fitaccen dan wasan kwallon kafa na kasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya zama gwarzon dan wasan karni a bikin ba da lambar yabo ta ‘Globe Soccer Awards’.

Dan wasan gaban wanda a yanzu yake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Juventus, ya karbi kyautar ce da kansa a wani biki da aka gudanar ranar Lahadi a Otal din Armani da ke birnin Dubai.

Hakan na nufin Ronaldo ya zama zakaran gwajin dafi wanda ya yi wa dukkanin sa’o’insa masu buga tamola zarra a tsakanin shekarar 2001 zuwa 2020.

Zakakurin dan wasan ya yi wa wasu fitattun ’yan wasa fintinkau wajen lashe wannan gasa da suka hadar da Ronaldinho Gaúcho, Mohammed Salah da kuma babban abokin hamayyarsa wato Lionel Messi.

Ronaldo ya samu nasarar lashe wannan gagarumar kyauta ta bajimin dan wasa mafi kyau da nuna bajinta tsakanin shekarar 2001 zuwa 2020, bayan ya lashe Kofin Zakarun Turai guda biyar, Firimiyar Ingila uku tare da Manchester United, La Liga biyu a zaman da ya yi a Real Madrid Serie A biyu a Juventus da kuma Nations League tare da kasarsa ta Portugal.

Dan wasan mai shekaru 35 wanda ya lashe kyautar Balon d’Or sau biyar, ya yi alfahari da karbar wannan lambar yabo da cewa “ba don gwargwarmayar da na yi a manyan kungiyoyi ba, da samun kwarewa wajen manyan masu horaswa, da ban samu wannan kyauta ba.”

“Ba abu ne mai sauki ba yadda na kasance tauraruwata na kara haske a kullum tsawon shekaru da dama, saboda haka ina alfahari kuma ina godiya dangane da duk wata gudunmuwa da na samu a kwallon kafa musamman daga wajen masu horaswa da manyan kungiyoyin da na taka wa leda wajen kara min karfin gwiwa don na ci gaba da jajircewa.”

“Ina godiya ga duk wadanda suka zabe ni, iyalina, mahaifiyata da kuma ’yan uwana domin kuwa wannan nasara ce ta kwarai da za ta kara min karfin gwiwa na ci gaba da dagewa.”