✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Cristiano Ronaldo ya ci wa Portugal kwallo 101

Dan wasan Portugal da Juventus, Cristiano Ronaldo ya zura kwallo biyu a wasansu da Sweden a Gasar Kasashe wato Nations League, inda Portugal ta lashe…

Dan wasan Portugal da Juventus, Cristiano Ronaldo ya zura kwallo biyu a wasansu da Sweden a Gasar Kasashe wato Nations League, inda Portugal ta lashe wasan da ci biyu da nema.

Kwallon da ya zura na farko ne kwallonsa na 100, sai na biyu na zama na 101 a kasarsa ta Portugal.

Da wannan, dan wasan mai shekara 35 ya zama na biyu a tarihin kwallon kafa wanda ya zura kwallo 100 bayan tsohon dan wasan Iran Ali Daei, wanda ke da kwallo 109.

A wani tarihin daban kuma, Ronaldo ya zura kwallo 57 daga bugun tazara.

Ronaldo ya kwashe wata 10 yana da kwallo 99, tun bayan da ya zura kwallo na 99 a wasa tsakanin Portugal da Luxamburg a watan Nuwamban bara, inda ya zura kwallo daya bayan ya zura kwallo uku rigis a wasansu da Lithuania kafin wannan.

Gasar Kasashen ta bana, Ronaldo da Portugal suna neman kare martabarsu ne domin kare kambunsu bayan lashe gasar a karon farko da aka fara a bara, inda suka doke Netherland da ci daya da nema a wasan karshe.

Ronaldo ya zura kwallonsa na farko a Portugal ne yana da shekara 19 a gasar Nahiyar Turai ta shekarar 2004, sannan tun daga wancan lokacin, bai tsaya ba, har zuwa yanzu.

Kafin Ronaldo, dan wasan Portugal Pauleta ne ke rike da tarihin wanda ya fi kwallaye a kasar Portugal da kwallo 47.

Tuni tsohon dan wasan Brazil, Pele ya aika masa sakon taya murna, inda ya ce, “A yanzu Ronaldo ne dan wasan da ya fi kwazo.

“Na yi tunanin yau za mu taya shi murnar samun kwallo 100 ne, ashe murnar kwallo 101 za mu yi. Ina maka murna”, inji Pele wanda shi ma ya zura kwallo 77 ga kasarsa Brazil.

A daya bangaren kuma, dan wasan Ajantaina da Barcelona, Lionel Messi ya zura wa kasarsa kwallo 70 ne.