A yayin da masu iya magana kan ce ‘tururuwa ba ta gudun magana’, hakan ta ke ga dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Cristiano Ronaldo, a yayin da a ranar Laraba ya zura kwallo ta 750 a tarihinsa na fagen sana’ar tamola.
Kafa sabon tarihin zura kwallaye 750 da Ronaldo ya yi ya zo ne a wasan karawar da kungiyarsa ta Juventus ta yi a gasar Kofin Zakarun Turai da kungiyar Dynamo Kyiv a ranar Laraba.
- ‘Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun yi garkuwa da 5 a Neja
- Shekarau ya kalubalanci Buhari kan kin sauke manyan Hafsoshin Tsaro
- Manoma sun bukaci gwamnati ta biya diyyar takwarorinsu da aka kashe a Borno
Ronaldo bayan an tashi wasan cikin wani sako da ya wallafa a shafukansa na dandalan sada zumunta, ya ce fatan shi ne ya cike yawan kwallayen da ya zura zuwa 800 cikin dan takaitaccen lokaci.
Kwallo daya tilo da Ronaldo ya sakada cikin sauki a wani yanayi da ‘yan hausa ke kira ‘daga buhu sai tukunya’ a minti na 57, ta zamo kwallo cikon ta 75 da ya jefa a kungiyar Juventus tun bayan zuwansa shekaru biyu da suka gabata.
Alkaluma na tarihi sun nuna cewa a yanzu Ronaldo mai shekaru 35 a duniya, ya zura kwallaye 450 a tsawon shekaru 9 da ya shafe yana taka leda a kungiyar Real Madrid.
Dan wasan ya kuma zura kwallaye 118 a zaman da ya yi a kungiyar Manchester United.
Har ila yau, Ronaldo shi ne dan wasan da ya fi kowa yawan kwallaye a kasar Portugal, inda tun daga shekarar 2003 har zuwa yanzu, ya zura wa kasar kwallaye 102.
Haka kuma, zakakurin dan wasan ya zura kwallaye 5 ga kungiyarsa ta farko, wato Sporting, wadda ta fara haska shi a duniya har ya zamo abin da ya zama a yanzu.
Jaridar hikaito labaran wasanni ta Goal.com, ta ce Ronaldo na daga cikin ’yan wasa hudu da suka jefa kwallaye sama da 500 a koma, inda sauran da suka yi wannan fice suka hadar da Lionel Messi, Robert Lewandowski da kuma Zlatan Ibrahimovic.
A yayin da ‘idan a na dara fidda uwa ake’ Ronaldo da Lionel Messi ne kadai ke tututiya ta shiga sahun ’yan wasa da suka zura kwallaye sama da 700 a koma.