Sabon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr da ke Saudiyya, Cristiano Ronaldo na son kungiyar ta shiga zawarcin tsohon abokinsa, Pepé.
Ronaldo da Pepé abokai ne tun tali-tali, wanda suka doka wa Portugal wasa tare kafin daga bisani su sake haduwa a Real Madrid, inda suka shafe shekaru tare.
- Ganduje zai tantance jam’iyyu kafin kamfe a filin wasa na Sani Abacha
- Borno ta Tsakiya: Kotu ta soke dan takarar Sanatan PDP
Pepé wanda a yanzu yake tare da kungiyar kwallon kafa ta FC Porto da ke kasar Portugal, zai cika shekara 40 a duniya a wata mai kamawa.
Al-Nassr dai ta shirya yin cefane don daga darajar gasar Saudiyya, wanda hakan ya sa aka fara rade-radin tana zawarcin tsohon kyaftin din Real Madrid, Sergio Ramos, Luka Modric da kuma Eden Hazard.
Ronaldo ya sanya wa Al-Nassr hannu bayan warware kwantaraginsa da Manchester United, lamarin da ya sa ya fi kowane dan wasa a duniya daukar albashi.
Zuwan Ronaldo Al-Nassr ya sauya fasalin yadda gasar Saudiyya ke tafiya, tuni masu ruwa da tsaki da ’yan kasuwa suka fara sanya kudi a gasar.