✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronaldo da Messi da Manuel Neuer ne za su fafata a gasar Gwarzon dan kwallon Duniya

 A ranar Talatar da ta gabata ne Hukumar shirya kwallo ta duniya (FIFA) ta fitar da sunayen ’yan kwallo uku da za su fafata a…

 A ranar Talatar da ta gabata ne Hukumar shirya kwallo ta duniya (FIFA) ta fitar da sunayen ’yan kwallo uku da za su fafata a gasar gwarzon dan kwallon duniya da ake wa lakabi da Ballon d’Or.
Za a gudanar da gasar ce a ranar Litinin 12 ga watan Janairun 2015 a hedkwatar hukumar da ke Zurich na kasar Suwizilan idan Allah Ya kaimu.
An tantance ’yan kwallo uku ne daga cikin 23 da za su fafata a gasar.  ’Yan kwallon da aka zabo sun hada da Cristiano Ronaldo wanda ke kwallo a kulob din Real Madrid da ke Sifen kuma haifaffen Fotugal kuma shi ne ya lashe gasar a bara.  Idan ya sake lashe ta bana kenan zai lashe sau uku kenan.  Ya taba lashewa a lokacin da yake buga wa kulob din Manchester United na Ingila kwallo yayin da ya sake lashe ta a bara a kulob din Real Madrid na Sifen to idan ya sake samun nasara a wannan karo za a iya cewa ya lashe sau uku a kulob daban-daban kenan.  An zabo shi ne bayan ya kafa tarihin dan kwallon da ya fi zura kwallaye a raga a gasar zakarun kulob-kulob na Nahiyar Turai (UEFA Champions League) bayan ya zura kwallaye 17 sannna ya taimaka wa kulob din Madrid lashe kofin na Champions League karo na 10 da kuma kofin Sarki (Kings Cup).
Sai na biyun dan kwallon da aka zabo, watau Lionel Messi, dan kwallon FC Barcelona na Sifen kuma haifaffen Ajantina.
Messi ya kafa tarihin lashe gasar har sau hudu a jere.  Duk da yake a bara kulob dinsa na FC Barcelona bai lashe kofi ko daya ba amma ya taimaka wa kasar Ajantina kaiwa wasan karshe a gasar cin kofin duniya da aka yi a Brazil bayan Jamus ta lasheta da ci 1-0 a wasan karshe.  Sannan Messi ne aka zaba a matsayin dan kwallon da ya fi nuna kwazo a gasar cin kofin duniya.  Dalilin da ya sa kenan aka zabe shi a matsayin daya daga cikin wadanda za su fafata a gasar.  Sannan a baya baya-bayan nan ya kafa tarihin dan kwallon da ya fi zura kwallaye a gasar rukuni–rukuni na Sifen watau La-Liga da kuma a gasar zakarun kulob-kulob na Nahiyar Turai (Champions League).  A gasar La-Liga kawo yanzu ya kafa tarihin zura kwallaye 253 yayin da a gasar Champions League kuma ya zura kwallaye 74.
Sai na ukunsu shi ne golan Jamus Manuel Neuer.  Shi ne golan da ya taimaka wa kulob din Jamus lashe gasar kofin duniya da aka yi a Brazil.  Sannan ya taimaka wa kulob din Bayern Munich wajen lashe kofuna biyu a Jamus.  Idan Neuer ya lashe gasar, zai kasance shi ne gola na biyu da ya taba samun nasarar zama gwarzon dan kwallon duniya baya ga golan Rasha Lebi Yashin da ya taba lashewa a shekarun baya.