✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronaldinhon ya yi ritaya daga kwallon kafa

Shahararren xan kwallon Brazil Ronaldinho a shekaranjiya Laraba ne ya bayar da sanarwar yin ritaya daga wasan kwallon kafa.  Ya bayar da sanarwar ce ta…

Shahararren xan kwallon Brazil Ronaldinho a shekaranjiya Laraba ne ya bayar da sanarwar yin ritaya daga wasan kwallon kafa.  Ya bayar da sanarwar ce ta hannun xan uwansa Roberto Assis. 

Xan kimanin shekara 37, Ronaldinho dai ya yi suna a fagen kwallon kafa musamman a lokacin da ya yi wasa a kulob xin FC Barcelona na Sifen.  

Ronaldinho ya buga wa kulob da dama a ciki da wajen Brazil.  Ya buga wa kulob xin PSG na Faransa ne a tsakanin shekarar 2001 zuwa 2003 daga nan ya koma kulob xin FC Barcelona a tsakanin shekarar 2003 zuwa 2008 daga nan ya koma AC Milan na Italiya a tsakanin shekarar 2008 zuwa 2011.  A shekarar 2004 ne ya lashe Gwarzon xan kwallon duniya (FIFA Ballon D’or).