✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Roman Reigns zai daina kokawa saboda cutar amosanin jini

Wani shahararren dan wasan kokawar Turawa dan asalin Amurka, Leah Joseph wanda aka fi sani da Roman Reigns ya fadi a ranar Litinin da ta…

Wani shahararren dan wasan kokawar Turawa dan asalin Amurka, Leah Joseph wanda aka fi sani da Roman Reigns ya fadi a ranar Litinin da ta wuce cewa zai daina  wasan kokawa saboda ya kamu da cutar amosanin jini (Leukemia).

Dan wasan, wanda ya lashe manyan gasannin kokawa a ciki da wajen Amurka ya ce kimanin shekara 11 da suka gabata ne likitoci suka ce akwai yiwuwar ya kamu da cutar amosanin jinin amma sai yanzu abin ya tabbata.

Ya ce duk wanda ya ga yadda yake kayar da maza a kokawa ya san shi lafiyayye kuma kwararre ne a wannan fanni, amma yanzu da ya kamu da wannan cuta, ya san hakan ba zai ba shi damar ci gaba da wasa ba.

Roman ya ce zai kyautar da duk lambobin yabon da ya samu a gasar, don ya nuna damuwarsa a kan abin da ya same shi.

Sai dai ya gargadi ’yan wasan kokawa na Amurka cewa kada su dauka ya daina yin kokawa ne kwata-kwata a rayuwarsa da zarar ya samu lafiya zai koma fagen fama.

“Ina sanar da ku daga yanzu na daina yin wasan kokawa saboda cutar amosanin jini da na kamu da ita, amma ba na daina wasan kwata-kwata ba ne, idan na samu sauki akwai yiwuwar na koma fagen wasa nan gaba,” inji shi.