✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Roma ta lashe gasar ‘Europa Conference League’

Wannan shi ne karo na farko da Roma ta taba lashe wani kofi makamancin wannan.

A ranar Laraba ce kungiyar kwallon kafa ta Roma da ke kasar Italiya, ta yi nasarar lashe kofin ta na farko na wasannin Turai.

Wannan ya biyo bayan doke Feyenoord da ci 1-0 a wasan karshe na ‘Europa Conference League’.

Wannan shi ne karo na uku da kungiyar ta taba kai wa wasan karshe na kofin gasar wasannin Turai da ake bugawa.

Idan za a iya tunawa a shekarar 1984 kungiyar ta taba kai wa zagaye na karshe a gasar Europa sai dai kuma ta sha kashi a hannun Liverpool.

Kazalika, shekaru bakwai da suka wuce ta kai wasan karshe ta kofin Europa, duk da haka ba ta yi nasara ba, sai ta kare a matsayi na biyu bayan ta sha kashi a hannun takwararta ta kasar Italiya, wato Inter Milan.

Dan wasan Roma Nicolo Zaniolo ne ya zura kwallon tilo a minti na 32 da fara wasan a ragar Feyenoord.

Dan wasan mai shekaru 22 da haihuwa, shi ne ya ci kwallo har sau uku a wasan kusa da na karshe da Roma ta buga da kungiyar Bodo/Glimt domin kai wa zagayen gaba, wanda wadannan kwallo ukun da ya zura a raga suka taimaka wa kungiyar domin kai wa zagayen kusa da na karshe.

Wannan dai shi ne kofi na farko da koci Mourinho ya ci wa kungiyar tun bayan zuwansa Roma.

%d bloggers like this: