✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikita-rikitar gwamnatin Tinubu a kwana 100

A kwanaki 100 na shugabancin Tinubu a Najeriya, rikita-rikita iri-iri ne suka dabaibaye gwamnatinsa

A yayin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cika kwanaki 100 a kan mulkin Najeriya, Aminiya ta zakulo muku wasu daga cikin rikita-rikitar da suka dabaibaye gwamnatinsa.

Ga wasu daga ciki:

• Rikicin cire tallafin mai: Cire tallafin mai da na ci gaba da tayar da kura, ganin yadda matakin ya sa farashin  abuwa tashin gwaron zabo, sakamakon ninkuwar farashin litar mai daga N195 zuwa 540 — kafin daga bisani ya kai N615.

Tsadar rayuwar ta sa ’yan Najeriya fatali da bayanin Tinubu na cewa gwamnatinsa za ta sarrafa kudaden da ake kashewa a kan tallafin wajen bunkasa bangarorin ilmi da kiwon lafiya da noma da gyara hanyoyi da kyautata sufuri da sauransu.

Tashin farashin abubuwa sakamakon janye tallafin ya sa kungiyar kwadago zanga-zangar da yajin aikin neman a dawo da tallafin ko a yi wa ma’aikata karin albashi daidai da yanayin da kasar ke ciki.

• Karin kudin manyan makarantu: Gaza cika wa malaman jami’o’i alkawarin da ta yi musu na kudin gudanarwa da ma alawus-alawus da gwamnatin Najeriya ta yi ya sanya jami’o’i da manyan makarantun Najeriyar suka ninka kudin rajista, wanda ya tunzura iyaye da su kansu daliban, sakamakon matsalolin koma bayan tattalin arziki da ake fama da shi.

Majalisar dattawa dai ta shiga lamarin, domin kauce wa zanga-zangar da daliban suka shirya, sai dai har zuwa wannan lokacin ba ta sauya zani ba , illa iyaka gwanatocin jihohi da al’ummar kasa da suka tallafa wa wasu daga cikin daliban.

• Ma’aikatar Tsaro a hannun su Matawalle: Nadin tsohon Gwamnan Jigawa, Badaru Abubakar da takwaransa na Zamfara, Mohammed Bello Matawalle a matsayin ministan tsaro babba da karami, ya janyo cece-kuce saboda kallon da wasu ke yi wa Badaru a matsarin mara kwarewa a bangaren, shi kuma Matawalle a matsayin wanda ya kasa magance matsalar ‘yan bindiga a jiharsa lokacin da yake gwammna.

Sai dai Badarun ya mayar da martini cewa kasancewarsa gwamnan Jigawa na tsawon shekaru takwas ya isa ya tabbatar wa masu shakku cewa ya samu gogewar da ta kamata.

• Nadin Wike Ministan Abuja: Hakazalika nasa tsohon Gwamnan Ribas, Nyesom Wike a matsayin ministan Abuja ya tada kura, kasancewarsa dan jam’iyyar adawa ta PDP da har zuwa yanzu bai sauya sheka ba.

Rantsar da Wike ke da wuya haramta yin tallace-tallace a Abuja, tare da zayyano wasu unguwannin sama 30 da zai yi wa rusau a birnin.

• Cire sunan Maryam Shetty a cikin ministoci: Wata takaddama da ta dauki hankali ita ce yadda Tinubu ya sauya sunan Maryam Shettima (Shetty) da Jihar Kano a jerin ministocinsa, bayan da ta hallara a harabar majalisa domin tantancewa, ya maye gurbinta da Mariya Mairiga.

Tun lokacin da aka sanar da sunan Shetty abin ya tada kura, saboda kallon da wasu Kanawa suke mata na wacce ba ta da kwarewa, amma cece-kucen bai hana majalisa ta gayyace ta domin tantancewa ba.

Sai dai a yayin da ita da ‘yan rakiyarta ke jira a yi mata iso zuwa cikin zauren majalisar domin tantancewa, majalisar samu wasikar Tinubu na maye gurbinta da tsohuwar kwamishinar ilimi mai zurfi ta Kano Mariya Mahmud Bunkure, wanda ya janyo wani sabon ce-ce-ku-ce.

An zargi tsohon gwamnan jihar,  kuma Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje da hannu a sauyin da aka yi, amma ya fito daga baya ya ce shi ya bada shawarar sauya ta, domin Mariya ta fita cancanta.

• Rashin tantance El-Rufa’i: Wata takaddamar da ta taso ita ce rashin tantance tsohon Gwamnan Kaduna Nasir ElRufai domin zama minista a gwamnatin Tinubu bisa bukatar hukumar tsaro ta DSS, wanda ya janyo ka-ce-na-ce.

Kafin nan, yanayin tambayoyi masu sauke da aka yi masa a yayin tantance shi na farko da ba kammala ba, ya tada kura.

Daga baya, El-Rufai ya sa labule da Tinubu a Fadar Shugaban Kasa, washegari kuma ya sanar cewa ya janye sha’awarsa ta zama minista, wanda shi ma ya bar baya da kura, inda wasu ke ganin ba don radin kansa ya bjanye ba, kuma da gayya aka hana shi saboda bangaranci.

• Yunkurin daukar matakin soji a Nijar: A ranar 26 ga watan Yuli ne sojoji a Nijar karkashin jagorancin Abdulrahmane Tchiani suka yi wa Shugaba Muhammad Bazoum juyin mulki, wanda Majalisar Dinkin Duniya da Amurka da Kungiyar Kasashen Turai da Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) la’anta.

Juyin mulki ya dugunzuma tunanin Tinubu kasancewarsa Shugaban ECOWAS, inda ya yi barazanar daukar matakin soji matukar sojojin Nijar ba su dawo da kasar kan turbar dimokuradiyya ba.

Furuci ya tada kura a Najeriya da Nijar, inda musamman ’yan Arewacin Najeriya suka hada iyaka da Nijar din suka yi tir da barazanar, tare da kiran ECOWAS karyar farautar turai da Faransa.

Manyan malamai da sarakuna dai sun yi kokarin shiga tsakani musamman ganin sojojin da suka yi juyin mulki sun ki sauraron wakilan da ECOWAS ta tura domin tattaunawa da su da farko.

Haka kuma domin mayar da martani ga ECOWAS din bayan Janye whtar lantarkin da Najeriya ke ba su, sojojin da suka kwaci mulkin sun kori Wakilin Najeriya da na Faransa da Amurka. Har yanzu dai wannan batun na ci gaba da daukar hankali kuma al`ummar kasashen Najeriya da Nijar sun zuba ido don gani yadda za a kare kan lamarin.

• Daidaita tsarin canjin kudi: Babban Bankin Najeriya (CBN) ya tayar da kura bayan da ya sanar da dunƙule tsarin canjin kuɗaɗen waje a wuri guda, sabanin yadda a baya ake da tsarin canji na hukuma, da kuma na bayan fage.

Hakan ya sa a hukumance darajar Dala ta yi mummunan tashi daga daga Naira 477 zuwa 750, duk da haka masana tattalin arziƙi na cewa hakan zai sanyaya gwiwar masu boye Dalar domin sayar da ita da zarar ta yi tashi.

• Dambarwar tsare Emefiele: A ranar 9 ga watan Yuni ne ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayyar ya sanar an dakatar da Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele domin a gudanar da bincike a kansa, wanda daga bisani Hukumar Tsaro ta DSS ta cafke shi, ta titsiye sanna ta gurfanar da shi a gaban kotu kan zargin badakalar kudade.

Da yake jawabi a wani taron zauren musayar ra’ayi da ’yan Najeriya mazauna kasar Faransa, Tinubu ya ce daga cikin dalilan tube Emefiele daga matsayinsa shi ne durkusar da bangaren harkokin kudi saboda dagula lamuran kasuwar canji.

Bayan gurfanar da shi kotu bisa zargin mallakar haramtattun makamai, amma ya musanta ya kalubalanci DSS ta kawo hujja.

A zaman ne kotu ta da belin sa tare bisa sharadin tsare shi a gidan yari har sai ya cika sharuddan belin, ta dage zaman.

Kafin jami’an gidan yari su tafi da shi ne jami’an DSS suka yi dambe da su a harabar kotu suka kwace shi suka kai ofishinsu, wanda haka ya jawo wa DSS Allah-wadai da zargin zubar da kimar Najeriya a idon duniya.

• Tallafin N8,000 ga talakawa: Sakamakon yawaitar korafin tsadar rayuwa a Najeriya bayan cire tallafin fetur Tinubu ya sha alwashin bai wa ’yan kasar masu karamin karfi miliyan 12 tallafin Naira dubu takwas kowanne a tsawon wata 6.

Sai dai tun kafin a je ko’ina ne ’yan kasar suka soma sukar tsarin, lamarin da ya tilasta masa jingine shi da nufin yi masa garambawul.

Wannan ya zo ne sa’o’i bayan ƙunigyar ƙwadago ta yi watsi da bukatarsa ta neman amincewar majalisar dokoki don karbar rancen naira biliyan 500 daga Bankin Duniya da nufin aiwatar da shirin da kungiyar ta kira na bogi da nufin sace dukiyar talakawa, su kuma masu kuɗi su ƙara kuɗancewa. Har zuwa wannan lokacin dai ana ci gaba da tafka muhawara kan batun.