✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Zariya: Kotu ta yi watsi da bukatar Zakzaky ta a sake shi

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ki amincewa da bukatar jagoran kungiyar Harkar Musulunci (IMN) ta mabiya Shi’a, Sheikh Ibrahim Zakzaky na a…

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ki amincewa da bukatar jagoran kungiyar Harkar Musulunci (IMN) ta mabiya Shi’a, Sheikh Ibrahim Zakzaky na a hanzarta sake shi daga tsarewar da Hukumar Tsaron kasa (DSS) ke yi masa cikin gaggawa. Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Alkalin Kotun Mai shari’a Okon Abang, wanda ya ki amincewa da bukatar a cikin mako daya ya ki amincewa da bukatun dan Majalisar Tarayya Abdulmumini Jubril na nema a hana majalisar dakatar da shi. Sannan wata bukata da ya ki amincewa da ita ita ce ta masu neman a dakatar da nada Manajan Darakta da kwamishinonin Hukumar Raya Yankin Neja- Delta (NDDC) da kuma karar da ta shafi mazabar dan Majalisar Tarayya na Oron. Mai shari’a Abang ya ce, ya kamata Zakzaky ya nemi amincewar kotun kan a saurari shari’ar a lokacin hutunta. Kuma ya ce mai karar ya gaza kai sammaci ga Hukumar DSS da Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya da Babban Lauyan Najeriya a matsayinsu na wadanda ake kara. Ya ce, babu bukatar yin gaggawa a cikin lamarin, don haka akwai bukatar mai karar ya isar da sammaci a kan wadanda yake karar. Alkalin ya ce, karar an shigar da ita ce da farko a gaban Mai shari’a Gabriel Kolawole bisa umarnin Babban Jojin Babbar Kotun Tarayya. Don haka sai Mai shari’a Abang, ya ce bukatar ba ta da hujja kuma ya yi watsi da ita. Lauyan Zakzaky, Abubakar Masha ne ya shigar da karar yana bukatar a bai wanda yake kare hakkinsa na dan Adam.