✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rikicin yankin Gulf: Saudiyya da Qatar sun sasanta

Kasar Saudiyya ta amince ta bude iyakokinta ga makwabciyarta, Qatar a wani mataki na daidaitawa a dambarwar siyasar da ta kai ga Saudiyya da kawayenta…

Kasar Saudiyya ta amince ta bude iyakokinta ga makwabciyarta, Qatar a wani mataki na daidaitawa a dambarwar siyasar da ta kai ga Saudiyya da kawayenta a yankin Gulf suka kaurace wa Qatar tare da sanya mata takunkumi.

A ranar Litinin Saudiyya ta bude tashoshin jiragenta da iyakokin ruwa da na kan tudu ga Qatar, kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Wajen Kuwait, ta sanar.

Ganduje: Shirin Shekarau da Kwankwaso na ta da kura kan 2023

Me ya sa El-Rufai bai yi ta’aziyyar Iyan Zazzau ba?

“Bisa Bukatar [Sarkin Kuwait] Sheikh Nawaf, an amince a bude iyakokin ruwa da na kan tudu da sararin samaniyan da ke tsakanin kasashen Saudiyya da Qatar daga yau da yamma,” Inji Ministan Harkokin Wajen Kuwait, Ahmad Nasser Al-Sabah a ranar Litinin.

A watan Yunin 2017 ne aka sa wa Qatar takunkumi tare da rufe dukkannin iyakokinta da kasashen Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Bahrain da Masar, wadanda ke zargin ta da taimakon ’yan ta’adda, da alakar kut-da-kut da Iran, da kuma bata huldar jakandanci da na tattalin arziki.

Qatar ta sha musanta zargin, tana mai cewa “babu adalci” a hukuncin da  kasashen suka dauka na yanke hulda da ita.

Tun lokacin kasar Kuwati take ta kai-komo domin ganin kasashen hudu sun sasanta da Qatar.

A watan Disamban 2020, Kungiyar Kasashen Yankin Gulf (GCC) ta gayyaci Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani zuwa babban taronta da za a yi a makon gobe a Saudiyya da nufin sasanta rikicin.

A ranar Litinin, Sarkin Qatar, ya samu takardar gayyatar a hukumance zuwa taron na GCC mai kasashe shida.

Yarima Mai Jiran Gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya ce taron zai “rungumi kowane bangare domin hadin kai da samun karin kafarin tunkarar kalubalen da ke fuskantar yankinmu”.