✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Ukraine na iya rikidewa zuwa Yakin Duniya na Uku — Rasha

Amma ta ce tana sa ran za a kawo karshensa ta yarjejeniyar zaman lafiya

Yayin da yau aka haura kwana 65 da fara yakin Rasha a Ukraine, Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergei Lavrov, ya sake gargadin cewa akwai hadarin yakin Ukraine na iya kaiwa ga Yakin Duniya na Uku.

Amma ya ce yana sa ran za a kawo karshensa ta yarjejeniyar zaman lafiya.

Da yake magana da kafafen yada labaran kasar Rasha, ya ce Mosko na son kauce wa abin da ya kira hadarin wucin-gadi na irin wannan rikici.

Mista Lavrov ya zargi NATO da shiga yakin, yana gargadin cewa kasarsa za ta kai wa ayarin kungiyar da ke kai makamai Ukraine hari ba kakkautawa.

Makonnin da suka gabata Shugaba Putin ya umarci sojinsa masu kula da nukiliya su kasance cikin shiri.

Amurka ta ce ba ta son shiga rikicin ta hanyar sanya sojojinta a ciki domin hakan na iya haifar da Yakin Duniya na Uku.

Sannan Ma’aikatar Tsaron Rasha ta yi ikirarin kashe sojojin Ukraine 500 a ranar Litinin da daddare yayin wasu hare-hare ta sama da ta kai a wurare 87 a Ukraine.

Bataliyoyin sojin Ukraine biyu da suke Kharkiv na cikin wuraren da rahotanni suka ce sojin Rasha sun kai wa hari.

Ma’aikatar ta wallafa wani bidiyo a shafinta na Intanet da ke nuna wuraren da dakarunta suka kwace daga hannun sojojin Ukraine.

Bidiyon ya kuma nuna tankokin yaki da wasu motoci. Bayanai sun ce sojin Rasha sun samu makamai da wasu takardu da sauran kayayyakin sojojin Ukraine a wuraren.

A wani labarin kuma Hukumar Kula da ’Yan gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta kara kiyasin da ta yi na mutanen da ake sa ran za su tsere daga Ukraine a bana sakamakon yaki, zuwa mutum miliyan takwas da dubu 300.

A kiyasin da ta yi a watan jiya, ta ce ’yan gudun hijira miliyan hudu ne za su bar kasar, sai dai tuni adadin ya zarta haka.

Zuwa yanzu, fiye da mutum miliyan biyar ne suka tsere daga kasar tun lokacin da Rasha ta kaddamar da yaki a kasar a watan Fabrairu, yayin da yakin ya raba karin mutum miliyan bakwai da dubu 700 da muhallansu.