✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rikicin Ukraine: Birtaniya ta kwace kadarorin Abramovich

Birtaniya ta kakabawa attajiran Rasha bakwai takunkumi.

Gwamnatin Birtaniya ta kara kafa kahon zuka ga mamallakin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Roman Abramovich a matsayin karin martaninta kan mamayar da Rasha ta yi wa kasar Ukraine.

Yana cikin manyan attajirai bakwai da Birtaniyar za ta kakaba wa sabbin takunkumai, ciki har da kwace kadarorinsa da kuma hana shi tafiye-tafiye.

Cikin attajiran da wannan matakin zai shafa akwai Igor Sechin da Oleg Deripaska, wadanda ake kallo a matsayin makusantan shugaban Rasha, Vladimir Putin.

Fira Ministan Birtaniya, Boris Johnson, ya ce, “babu maboya” magoya bayan mamayar Rasha a Ukraine.

Gwamnatinsa ta sha matsin lamba domin ta dauki mataki kan Mista Abramovich, wanda ya ce ya yanke shawarar sayar da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da ya mallaka a farkon wannan watan.

Ana hasashen Abramovich mai shekara 55, na hannun daman Putin ne, zargin da ya musanta.

An yi kiyasin dukiyar Abramovich ta kai fam biliyan 9.4.

Tuni kasashen Turai suka ci gaba da kakaba wa Rasha takunkumi kan hare-haren da ta kaddamar kan Ukraine.