Ofishin Jakadancin Najeriya a kasar Ukraine ya gargadi ’yan Najeriya mazauna kasar da su kiyayi yin tafiye-tafiye barkatai da kuma shiga yankunan da ke fama da rikici a kasar.
A shekarar da ta wuce, Shugaban Kungiyar Daliban Najeriya a Ukraine, Martin Dele Lawani, ya bayyana cewa ’yan Najeriya akalla 8,000 ne suke karatu da kuma kasuwancinsu a Ukraine.
- NAJERIYA A YAU: Zaben 2023: Wa zai kai Najeriya tudun mun-tsira
- Yadda za a yi buda baki a masallacin Annabi a watan Azumin bana
Kwanaki uku suka wuce, Birtaniya ta ba da umarnin janye ma’aikatan ofishin jakadancinta da ke kasar kan fargabar yiwuwar hari daga kasar Rasha a kowane lokaci.
Wata sanarwa da aka fitar ga ’yan Najeriyar ta ce, “Ana jan hankalin ’yan Najeriya da cewa duk inda za su je su kasance dauke da katin shaidarsu.
“Ana kuma shawartar ’yan Najeriya mazauna Ukraine da su tuntubi Ofishin Jakadancin Najeriya game da karin bayani kan halin da ake ciki a kasar nan game da sha’anin tsaro.”