✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Tigray: Jiragen yaki sun kashe mutum 10 a yankin Mekele

Tagwayen hare-haren jiragen yaki sun kashe akalla mutum 10 a yankin Tigray da ke kasar Habasha ranar Laraba.

Tagwayen hare-haren jiragen yakin gwamnatin Habasha sun kashe fararen hula 10 a yankin Tigray da ke kasar a ranar Laraba.

Harin dai na zuwa ne bayan hukumomin kasar sun amince da tsagaita wuta.

Wani babban jami’i a babban asibitin Tigray na Ayder, Kibrom Gebreselassie, ya ce an kai hare-haren a wata unguwa da ke yankin Mekele, inda mutum 10 suka rasu, wasu da dama suka jikkata.

Wani babban likitan tiyata a asibitin ya ce harin farko ya raunata wasu mata biyu, na biyun kuma ya fada kan wadanda suka suka taru domin taimakawa wadanda harin farkon ya afkawa.

“A cikinsu wani magidanci ya mutu, yayin da dansa kuma ya samu mummunar raunin da sai da aka yi masa tiyata,” in ji.

Tun da fari dai mai magana da yawun kungiyar ’yan tawayen Tigray (TPLF) da ke yaki da gwamnatin Habasha kusan shekaru biyu, ya ce an kashe fararen hula da raunata da dama a harin.

Amma bai yi karin bayani kan hakan ba.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya ce, har yanzu bai iya tabbatar da ikirarin ba, sakamakon tsaurara matakan shiga yankin Arewacin Habashan da aka yi, sannan hanyoyin sadarwar Tigray a katse suke sama da shekara guda.