✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Tibi da Jukun ya sake yaduwa a Donga da Takum a Taraba

A rikicin da ake yi tsakanin kabilun Tibi da Jukun da ya ki ci ya ki cinyewa a jihar Taraba, a yanzu haka ya sake…

A rikicin da ake yi tsakanin kabilun Tibi da Jukun da ya ki ci ya ki cinyewa a jihar Taraba, a yanzu haka ya sake yaduwa zuwa wasu yankunan Kananan Hukumomin Donga da Takum yayin da wasu  mafusata suke kai hari unguwannin Tibi.

A binciken majiyarmu an kona gidaje da dama a wasu kauyukan Tibi da ke cikin Kananan Hukumomin Donga da Takum, wanda hakan ya tilastawa wasu mata da yara barin garuruwan.

Rikicin dai ya fara ne a tsakanin kabilun Tibi da Jukun daga Karamar Hukumar Wukari sama da wata daya da wuce wanda ya yi sanadiyyar rasa rayuka da dukiyoyin na Miliyoyin Naira.