✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin shugabanci ya kunno kai a Kasuwar Kwari

Rikicin Shugabanci a Kasuwar Kantin Kwari yana neman raba kasuwar zuwa bangarori biyu, inda wasu ke goyon bayan shugabanni masu ci tare da fatan dorewar…

Rikicin Shugabanci a Kasuwar Kantin Kwari yana neman raba kasuwar zuwa bangarori biyu, inda wasu ke goyon bayan shugabanni masu ci tare da fatan dorewar shugabancinsu a gefe guda, sai bangaren da ke neman canjin shugabancin kasuwar. 

Kimanin shekaru hudu ke nan da shugabanni karkashin jagorancin Alhaji Liti Jibrin kulkul ke jan ragamar shugabancin kungiyar.
Aminiya ta zaga cikin kasuwar, inda ta ji ra’ayin wasu ’yan kasuwa game da wanann tirka-tirka da ta kunno kai kasuwar, wadda ta yi fice a kasuwancin kayan da suka shafi sutura.
Malam Mika’ila Haruna dan kasuwa ne a kasuwar kuma ya bayyana cewa: “Muna son samun canjin shugabancin ne sakamakon rauni da shugabancin na yanzu yake da shi. Raunin ya hada da rashin biyan ma’aikatan tsaro alawus dinsu a kan lokaci. Ina ganin shi kuwa sha’anin shugabancin kowane iri ne dole ne a samu jajircewa a cikin gudanar da shi idan har ana so a samu nasara,” inji shi.
Kodayake Mustapha Rijiya Biyu Goron Dutse cewa ya yi bai ga wani abu na cikas dangane da shugabancin kungiyar kasuwar ba, a cewarsa “shugabannin na yanzu suna kokari wajen samar da ingantaccen tsaro a kasuwa da kuma kula da sha’anin tsaftar kasuwa,” inji shi.