✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Sasa: Kotu ta bada umarnin tsare mutum bakwai 

’Yan sanda na zarginsu da hannu a mutuwar wasu mutum 31.

Wata Kotun Majistire da ke zama a yankin Iyagakun na birnin Ibadan a Jihar Oyo, ta bayar da umarnin tsare wasu mutum bakwai da ake zargi da tayar da hargitsi gami da kisan kai a yayin rikicin da ya barke a kasuwar Sasa.

Wadanda ake zargin sun hadar da Tajudeen Oladunni mai shekaru 50 sai Saburi Lawal mai shekaru 37 da Ojo Joshua mai shekaru 25 sai Adekunle Olanrewaju mai shekaru 38 da Olagunju James mai shekaru 24 sai Rasaq Yahya mai shekaru 32 tare da Olaide Olawuyi mai shekaru 20, kuma rundunar yan sanda tayi karar su ne a kan laifuka shida da ake zargin su da aikatawa da suka hadar da tayar da tarzoma da kisan kai.

Mai shari’a I.O Osho ta yi watsi da neman afuwar wadanda ake zargin inda a ranar Alhamis ta bada umarnin ci gaba da tsare su a gidan gyara halin, ta kuma bai wa ’yan sanda umarnin a mayar da takardun karar su zuwa ga babban Darakta na sashen ladabtarwa domin ya bada shawara game da shari’ar.

Aminiya ta samu cewa, Mai Shari’a Osho ta kuma dage sauraron karar zuwa ranar 11 ga watan Mayu.

Tun da fari dai lauyan da ya shigar da karar, Foluke Oladosu, ya shaida wa Kotun cewa wadanda ake zargin tare da wasunsu da suka tsere ne suka aikata laifin.

Ya ce da misalin karfe 10 na safiyar ranar 12 ga watan Fabrairun 2021 ne wadanda ake zargin suka yi sanadiyar mutuwar wani Adeola Shakirudeen, a unguwar Sasa da ke birnin na Ibadan bayan sun rufe shi da duka.

Bugu da kari, ’yan sanda na zarginsu da hannu a mutuwar karin wasu mutum 31 tare da sanya wuta a gidaje biyu mallakin wani mai suna Ibrahim wanda hakan ya haddasa masa asarar naira miliyan hamsin.

Kazalika, ’yan sanda na zarginsu da kona wani gida mallakar wani mutum mai suna Osuolale Akindele tare da lalata dukiya ta kimanin naira miliyan ashirin.

Dan sanda mai shigar da karar ya ce laifin da ake zargin su da aikata wa ya saba wa sashi na 6 da 316 na kundin dokokin manyan laifuka na jihar Oyo wanda za a hukunta duk wanda aka samu da laifin a karkashin sashi na 319 da na 516 na kundin dokokin manyan laifuka na Jihar.