Rabilu Abubakar, Gombe
Bayan rasuwar Mai Tangle Dokta Abdu Buba Mai Sheru III, rikici kan nadin sabon Mai Tangale na 16 da zai gaje shi ya fusata yan kabilar Tangale inda matansu da yara kanana suka fito suna bore tare da rufe babbar hanyar Gombe zuwa Yola.
Masu Zanga-zangar sun nuna rashin amincewarsu da zabin sarkin da ake cewa gwamnan jihar ya yi wanda a cewarsu ba shi ne zabinsu ba, kuma bai kamata gwamnati ta yi musu shisshiga ba, a nada musu wanda suke so kawai.
Hakan tasa dan Majalisar Tarayyar mai wakiltar Billiri da Balanga, Victo Mela Dan Zaria da yan majalisa biyu na jiha Rambi Ibrahim Ayala da Rabaren Tlfukut Kardi daga Billiri ta Gabas da Yamma suka nemi shiga garin don kwantar wa da masu boren hankali amma suka hana su shiga garin.
Da Aminiya take zantawa da Victor Mela Danzaria kan lamarin, sai ya ce sun yi kokarin shiga Billiri ne shi da ‘yan Majalisuarsu ta don shawo kan rikicin amma masu zanga-zangar suka hana su shiga suka ce su koma ba su yarda da su ba.
Victor Mela, ya ce matan da yara da suka fito kan titi suna kwana a boren da suke yi saboda nuna fushinsu ga gwamnati ba su san cewa sun zo su yi musu bayanin halin da ake ciki ba ne.
A cewarsa, sun je wani gari mai suna Ladongur kusa da Billiri amma masu boren suka ce sam ba su yarda su wuce ba, hakan ta sa dole suka juyo suka dawo Gombe za su sake shawari suga ya za’ayi.
Daga nan sai ya yi kira ga Gwamnatin Inuwa Yahaya da cewa ta gaggauta nada musu sarkin da suke so, domin yin hakan ne zai kawo karshen rikicin da ta shafi matafiya a kan hanya inda manyan motoci fiye da 200 suka tsaya a garin Kumo ba gaba ba baya saboda ba yadda za a yi su wuce zuwa Adamawa ko Taraba.