Fustattun matasan sun kona fadar Oba Ponle Ademola da ke garin na Boripe ne bayan jami’an tsaro sun tsare wani basarake, Aogun na Iree, Cif Soliu Atoyebi, a safiyar ranar.
Masu tarzomar sun toshe manyan titunan shiga garin suna kona tayoyi a kan hanyoyim.
Ganin haka ne ’yan kasuwa suka rufe kantunansu, a yayin da mazauna garin suka shige gidajensu domin kada rikicin ya shafe su.
Takaddamar sarauta
Ba a samu kakakin ’yan sanda ta Jihar Osun ba, SP Yemisi Opalola, domin samun karin bayani, saboda wayarta na kashe.
A ranar Litinin, washegarin rantsar da sabon Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya soke nadin wasu sarakuna uku: Aare na Iree da Akirun na Ikirun da kuma Owa na Igbajo.
Gwamnan Adeleke ya umarci jami’an tsaro su garkame fadar sarakunan, su ci gaba da kula da su domin dakile duk wata tashin-tashina.
Mazauna garin Iree dai sun kasance cikin zullumi tun bayan nadin Prince Ponle Ademola a matsarin Aree na Iree, da tsohon gwamna, Gboyega Oyetola, ya yi kafin saukarsa daga mulki.
Tun a lokacin, wasu kungiyoyi da gidajen sarauta suka nuna adawarsu da nadin Prince Ademola, wanda suka ce dauki-doransa jami’an Gwamnatin Oyetola suka yi musu.