✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Sarauta: Alkalan Kano za su gurfana a Abuja kan umarni masu karo da juna

Babban Alkalin Kas ya bukaci shugabannin kotunan da suka yanke hukunce-hukunce masu karo da juna a Shari'ar Sarautar Kano su bayyana a gabansa domin amsa…

Babban Alkalin Najeriya, Mai Shari’a Olukayode Ariwoola, ya umarci shugabannin kotunan da suka yanke hukunce-hukunce masu karo da juna a Shari’ar Dambarwar Sarautar Kano su gurfana a gabansa domin amsa tambayoyi.

A ranar Laraba kakakin babban alkalin, Soji Oye, ya sanar da haka, a daidai lokacin da ake ci gaba da kai ruwa rana kan halascin tube Sarki Aminu Ado Bayero da kuma nada Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16 da gwamnatin jihar ta yi.

A ranar ce kuma gwamnatin jihar ta ba da umarnin kama masu gudanar da zanga-zanga ko tarukan jama’a masu alaka da rikicin.

Sanarwar ofishin babban alkalin ta bayyana cewa wadansa da za su gurfana su ne Babban Alkalin Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano da kuma takwaransa na Babbar Kotun jihar.

Manyan alkalan za su amsa tambayoyi a gaban babban alkalin kasar ne kan hukunce-hukunce masu karo da juna da kotunansu suka yanke a ranakun 24, 28 da kuma 28 ga watan Mayu, 2024, kan dambarwar masarautun Kano.

Ana iya tunawa a ranar 25 ga watan Mayu Mai Shari’a Abdullahi M. Liman na Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ya ba da umarnin dakatar da gwamnatin jihar daga rushe masarautun jihar biyar da tsohuwar gwamnatin jihar karkashin Abdullahi Ganduje ta kirkiro.

Umarnin kotun ta kuma hana aiwatar da sabuwar dokar masarautun jihar wadda ta kai ga nada Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon Sarkin Kano, tare da tube Aminu Ado Bayero.

Daga bisani Mai Shari’a Aminu Adamu na Babbar Kotun Jihar Kano ya ba da umarnin hana hukumomi yin wata barazana ga Sanusi II.

Daga baya kuma wani Mai Shari’a S. A. Amobeda, ya ba da umarnin fitar da Sanusi II daga Fadar Sarkin Kano ta Kofar Kudu, domin ba wa Aminu wurin gudanar da harkokin sarauta.

A nata bangaren, Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) ta yi tir da abin da kotunan suka yi.

Shugaban kungiyar lauyoyin, Yakubu Maikyau (SAN), ya bayyana cewa abin da kotunan suka yi bai dace ba kuma zubar da mutuncin bangaren shari’a ne.

Maikyau ya ce babu wani abin daure kai da zai sa aljalai da lauyoyin bangarorin da ke shari’ar su yi wannan kwamacala alhali a baya an riga an yanke hukunci kan irin wannan al’amari.

Don haka ya bukaci hukumar sharia da ta gudanar da bincike tare hukunta duk wanda aka samu da laifi.