Birtaniya ta yi tayin tura sojojin kasa da na sama da na ruwa don karfafa tsaron iyakokin Gabashi da Arewacin kasashe mambobin kungiyar tsaro ta NATO yayin da ake kara tayar da jijiyoyin wuya a kan take-taken Rasha game da Ukraine.
A wannan makon ne dai ake sa ran Firayim Ministan Birtaniyar, Boris Johnson, zai magana da Shugaba Vladimir Putin na Rasha, sannan ya ziyarci yankin, duk kuwa da takaddamar da ta dabaibaye shi a cikin gida.
- ’Yan bindiga sun hallaka mutane da dama, sun kone gidaje a Neja
- Ta rayu shekara 20 da almakashi 2 da likitoci suka manta a cinkinta
Mista Johnson ya ce aikewa da karin sojojin alama ce ta kudurin Birtaniya na karfafa zumunci da kawayenta na yankunan Baltic da Nordic.
A wata sanarwa da ya fitar, Firayim Ministan na Birtaniya ya ce manufar shawarar ita ce “aikewa da sako mai karfi ga Rasha”.
“Ba za mu nade hannu ba muna kallo suna kokarin ta da zaune tsaye, kuma a kullum za mu mara wa kawayenmu na NATO baya idan suna fuskantar musgunawa daga Rasha”.
Matakin dai ya hada da tura jiragen ruwa na yaki biyu Bahar Aswad, da kara yawan sojoji da girke rokoki a Estoniya – a kan iyakar kasar da Rasha – da kuma aikewa da jiragen saman yaki don su rika shawagi a sararin samaniyar Romeniya da Bulgeriya daga wani sansani a Cyprus, inji Ma’aikatar Harkokin Waje ta Birtaniya.
A wannan makon jami’an Birtaniya za su je Brussels don daddale abubuwan da za a aika.
Boris Johnson ya bukaci shugabannin hukumomin tsaro na Birtaniya su kara zage dantse a Turai, sannan ya umarci ministocinsa na tsaro da harkokin waje su tafi Moscow domin ganawa da takwarorin aikinsu na Rasha.
A ranar Talata ake sa ran Babban Hafsan Hafsoshin Tsaro na Birtaniya, Admiral Sir Tony Radakin, zai yi jawabi ga majalisar ministocin kasar a kan rikicin na Ukraine.